Legit Hausa
A yau Talata kungiyar Jakadun
Najeriya reshen jihar Benuwe, ta jaddada bakuta gami da muhimmancin soke
maimaicin zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 23 ga watan Maris kamar
yadda hukumar zabe ta kayyade. Da ta ke gabatar da jawabai yayin ganawa da
manema labarai cikin birnin Makurdi, kungiyar ta yi kira ga shugaban kasa
Muhammadu Buhari da ya shiga cikin lamarin maimaicin zaben gwamnan jihar Benuwe
da ka iya tayar da zaune tsaye cikin ta da kuma kasa baki daya.
Tsohon jakadan Najeriya a kasar
Canada da kuma Mexico, Ambasada Iyorwuese Hagher da ya yi jawabi a madadin
sauran tsaffin Jakadu hudu na jihar Benuwe, ya gargadi shugaba Buhari akan
gaggawar shiga tare da yin ruwa da tsaki cikin zaben jihar Benuwe domin gudun
da na sani.
Ba ya ga kira na neman soke maimacin
zaben gwamna, kungiyar a nemi shugaba Buhari da ya shawarci hukumar INEC kan
tabbatar da gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom a matsayin wanda ya yi nasara
yayin zaben da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris.
Kungiyar ta yi tuni da cewa,
kasancewar su jakadu akwai bukatar shugaban kasa Buhari ya yi azama wajen kare
martaba da kuma 'yancin al'ummar jihar Benuwe ta hanyar ba su dama wajen zaben
shugabannin daidai ra'ayi domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Bayan zaben gwamnan jihar da aka
gudanar a ranar 9 ga watan Maris, gwamna Ortom na jam'iyyar PDP ya samu
gamayyar kuri'u 410,576 yayin da abokin adawar sa na jam'iyyar APC, Emmanuel
Jime ya samu kuri'u 339,022.
A yayin da akwai tazara ta kimanin
kuri'u 81,554 a tsakanin su, hukumar zabe ta ce zaben bai kammala ba a
sanadiyar adadin kuri'u 121,019 da ta soke da ka iya sauya sakamakon sa tare da
kaddamar da hukuncin maimaici a wannan mako.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI