Legit Hausa
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu
Buhari yayi fatali da wasu kudurorin dokoki guda biyu da majalisar tarayya suka
kai masa domin ya sa masu hannu, kamar dai yadda kakakin majalisar wakilan,
Yakubu Dogara ya bayyana a zauren majalisar ta wakilai.
Kudurorin da shugaban kasar ya
wancakalar din dai sun hada da na kafa wata cibiya da zata rika koyar da
hanyoyin lalubo matsaloli da kuma gyaran Najeriya watau Chartered Institute of
Training and Development of Nigeria.
Abun-da-babba-ya-hango: Buhari yayi
fatali da kudurorin doka 2 daga majalisar tarayya Abun-da-babba-ya-hango:
Buhari yayi fatali da kudurorin doka 2 daga majalisar tarayya Source: UGC Haka
ma dai shugaban kasar ya yi fatali da saka hannu a kan dokar da ta shafi kafa
wata manazartar harkokin aikin ceto na sararin samaniya watau Nigerian
Aeronautic Research Rescue Bill.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa ba
wannan ne karon farko ba da shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya ki sa wa wani
kuduri daga majalisar hannu ba a 'yan kwanakin nan. A kwanan baya ma dai
shugaban kasar ya yi fatali da wani kudurin da yayi gyare-gyare a harkokin
zabe.
A wani labarin kuma, Hukumar
gwamnatin tarayya dake yaki da masu laifuka da suka jibanci damfara watau
Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPS) ta
shirya kwace wasu filaye da gine-gine da suka kai darajar Naira biliyan 4.8
daga kamfanoni akalla 30.
Hukumar ta ICPC ta ce za ta kwace
kadarorin ne daga hannun masu su saboda karar da aka kai masu na kin biyan
harajin da ya kamata su biya na tsawon lokaci kamar dai yadda doka ta tanada.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi