Gwamnatin tarayya ta saka sharadin biyan sabon albashi na N30,000


Legit Hausa

Ministan Kasafin Kudi da Tsatsare na Kasa Sanata Udo Udoma ya ce gwamnatin tarayya tana tunanin kara harajin kayan masarufi domin ta samu ikon biyan sabon albashi mafi karanci na N30,000.

Udoma ya fadi hakan ne a ranar Talata yayin da ya bayyana a gaban kwamitin kudi majalisar dattawa.

Ministan ya kuma shaidawa kwamitin karkashin jagorancin Sanata John Owan-Enoh cewa kwamitin kwararu masu bayar da shawara a kan albashin mafi karanci za ta mika rahoton ta ga shugaba Muhammadu Buhari a cikin wannan makon.

Ya ce, "Albashi mafi karanci na N18,000 da ake biyan ma'aikata ya yi kadan sosai. Yana da matukar wahala ma'aikata su tafiyar da rayuwar su a kan wannan kudin.

"Shugaban kasa yana goyon bayan a sake duba batun albashin amma duk da hakan ya dace mu san cewa za mu iya biyan albashin.

"Saboda haka ne yasa muka zo wurin ku a majalisa domin akwai yiwuwar a yi wasu sauye-sauye musamman a harajin kayan masarufi saboda mu samu ikon cigaba da biyan albashin da zarar an zartas da shi.

" A yau Talata ne kuma majalisar dattawar ta amince da N30,000 a matsayin sabon albashi mafi karanci. An cimma wannan matsayar ne bayan kwamitin wucin gadi na sabon albashin mafi karanci karkashin Sanata Francis Alimikhena ta mika rahoton ta.

 DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN