Legit Hausa
A yau Alhamis cikin fadar Villa,
shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, kawowa yanzu akwai nauyi da
rataya a wuyan jam'iyyar adawa ta PDP dangane da yadda ta rike akalar dukiyar
kasar nan a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2014.
Mun samu cewa, a yau Alhamis
shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, kawowa yanzu jam'iyyar adawa ta
PDP ta gaza fayyace yadda tayi riko da akalar dukiyar al'ummar kasar nan tsawon
shekaru 16 da ta shafe a karagar mulki.
Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa,
shugaban kasa Buhari ya bayyana hakan ne a yau yayin karbar bakuncin
shugabannin kungiyar kwadago da suka ziyarce shi har fada domin taya murna ta
samun nasarar tazarce.
Cikin zayyana jawaban sa na takaici,
shugaban kasa Buhari ya ce gwamnatin sa ta riski kasar nan cikin wani
mawuyancin hali na mafi kololuwar durkuso musamman a fannin tabarbarewar
gine-gine.
Shugaba Buhari ya ce dole ne
gwamntin baya ta jam'iyyar PDP ta yi bayani dalla-dalla dangane da yadda ta yi
riko da akalar dukiyar kasar nan tsawon shekaru 16 da ta shafe a bisa kujerar mulki
yayin da kasar nan ta samu dumbin dukiya mafi yawa a tarihi ta hanyar arzikin
man fetur.
Yayin da ake ci gaba da fuskantar
karancin da rashin tsayayyar wutar lantarki a kasar nan, shugaba Buhari ya ce
ya gaza fahimtar yadda jam'iyyar PDP ta batar da Dalar Amurka Biliyan 16 akan
inganta wutar lantarki da kawowa yanzu ba bu amo ballantana labarin ta.
Shugaba
Buhari ya yi godiya da kuma jinjina ga jagorori na kungiyar kwadago sakamamakon
ziyarar taya murna da suka kawo masa har fada.
Ya yi kira na neman hadin gwiwar su
wajen ciyar da kasar nan gaba yayin jagoranci a wa'adin sa na biyu.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi