Type Here to Get Search Results !

Main event

Gwamna Abubakar bai amince ya sha kashi a zaben Bauchi ba tukun


Legit Hausa

Mai Gwamnan Jihar Bauchi, Muhammad Abubakar ya musanya rahotannin da ke yawo na cewa ya fito ya taya ‘dan takarar jam’iyyar PDP a zaben jihar watau Bala Mohammed murnar samun nasara. Gwamnan na Bauchi yayi wannan jawabi ne ta bakin babban Sakataren sa na yada labarai, Abubakar Alsadique.

Dazu aka rika jin labari na yawo cewa Gwamna Muhammad Abubakar ya saduda ya amince da shan kayi a zaben. Gwamnan yake cewa hankalin su ya zo kan wata jita-jita da ake yi na cewa har yayi maza ya taya Abokin hamayyar sa murna na lashe zaben da aka yi. Babban mai magana da yawun bakin gwamnan yace babu gaskiya a labarin.

Muhammad Abubakar ya musanya wannan rahoto da ya bi gari inda yace labari ne kurum irin na rediyo mai jini don haka yayi kira ga jama’a su yi watsi da wannan labari. Abubakar Alsadique yace sam bai fitar da wannan jawabi ba.

Mai magana da yawun bakin Gwamnan yace su na da hanyoyin ganawa da manema labarai idan har za a fitar da wani jawabi, inda yace a wannan karo gwamna bai zanta da ‘yan jarida, har yayi jawabin taya PDP murnar cin zabe ba.

Yanzu an koma cigaba da tattara sakamakon zaben da aka yi a cikin karamar hukumar Tafawa-Balewa da ta rage. A zaben cike-gibi da aka yi a Ranar Asabar, jam’iyyar PDP ce ta lallasa APC mai mulki a jihar.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies