Mubarak Idris na jam'iyar APC ya lashe zaben Gwamna a jihar Zamfara

Mubarak Idris na jam'iyar APC ya lashe zaben takaran kujerar Gwamna a jihar Zamfara. Mubarak ya sami kuri'a  34,541 daga cikin kuri'a 810,782 da aka kada a kananan hukumomi 14 da aka gudanar da zabe a jihar Zamfara ranar Asabar.

Shi kuma dan takarar jam'iyar PDP Bello Matawalle ya sami kuri'a 189,452.

Sanata Sa'idu Dansadau na jam'iyar NRM ya sami kuri'a 15,177 sai Abdullahi na jam'iyar APGA wanda ya sami kuri'a 3,865.

Baturen zabe na ajihar Zamfara Prafesa Kabir Bala ya ce akwai adadin mutum 1,717,128 da aka yi wa rijista, kuma aka tantance mutum 823,294 lokacin zaben.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

 Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post