Legit Hausa
Maryam Sanda, matar da ake zargi da
kisan maigidanta, Bilyaminu Bello, ta bayyanawa kotu cewa babu laifin da ta
aikata kan tuhumar da ake mata.
An gurfanar da ita tare da dan
uwanta Aliyu Sanda; mahaifiyarta, Maimuna Aliyu da mai aikinsu, Sadiya Aminu,
wadanda aka yiwa zargin taimakawa wajen boye hujja ta hanyar goge jinin
mamacin.
Yayinda aka koma shari'ar Maryam
ranar Talata, Lauyanta Olusegun Jolaawo, ya bayyanawa kotu cewa lauyoyin
gwamnati basu kawo kwararan hujjojin da zai bukaci ta kare kanta ba. Ya kara da
cewa duk hujjojin da lauyoyin gwamnati suka kawo an rigaya da watsi da su
lokacin da shaidu ke gabatar da shaidunsu.
Saboda haka, kotu ta wanke Maryam
Sanda daga zargin kisan kai. Hakazalika, lauyan mahaifiyar Maryam da dan uwanta
ya bukaci kotu ta sakesu saboda lauyoyin gwamnati basu kawo kwararan hujjojin
da zai bukacesu su kare kansu ba.
Amma lauyan gwamnati, Fidelis
Ogbobe, ya yi kirag kotun tayi watsu da wannan bukata da lauyan Maryam keyi.
Alkalin kotu, Jastis Yusuf Halilu, ya daga zaman zuwa ranar 4 ga watan Afrilu,
2019. Idan alkalin ya amsu bukatar lauyoyin dake kare wadanda ake zargi da
laifi, za'a sakesu.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI