Legit Hausa
A yayin ci gaba da kalubalantar
sakamakon zabe, Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar
PDP a zaben da aka gudanar na ranar 23 ga watan Fabrairu, ya gabatar da wani
sakamakon zaben da ya bankado shi daga yanar gizon hukumar zabe ta INEC.
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta
watau INEC ta tabbatar da nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar
APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar shugaban kasa da gamayyar kuri'u
15,191,847.
Sai dai yayin da hukumar INEC ta
tabbatar da shan kayen Atiku bayan ya lashe kuri'u 11,262,978, ya hau kujerar
naki ta amincewa da sakamakon zaben da cewar shi ke da rinjayen nasara da
kuri'u 18,356,732 yayin da a cewar sa Buhari ya samu kuri'u 16,741,430.
Duk da cewar sakamakon bai hadar da
kuri'un jihar Ribas ba, Atiku ya gabatar da wannan sakamako a gaban kotun
daukaka kara da ya yi ikirarin ya binciko ta barauniyar hanya daga ma'adanan
yanar gizo na hukumar INEC.
Binciken manema labarai na jaridar
Premium Times ya gano cewa, sakamakon zaben da Atiku ya gabatar cike ya ke da
kura-kurai da suka hadar da cewar takarar kujerar shugaban kasa ta gudana ne
kurum tamkar tsakanin sa da shugaba Buhari ba tare da sauran 'yan takara
kimanin 70 da suka fafata a zaben ba.
Cikin sakamakon zaben da Atiku ya
gabatar, ba bu kuri'a ko daya da aka soke cikin sakamakon zaben jihohi 33,
kazalika sauran 'yan takara 71 da suka fafata a zaben ba su samu ko da kuri'a
guda ba.
A jihohin Abia, Bauchi da kuma Cross
River, sakamakon zaben da Atiku ya gabatar na nuni da cewa adadin kuri'u da aka
kada tsakanin sa da shugaba Buhari sun haura adadi na yawan masu kada kuri'a da
hukumar INEC ta tantance.
A yayin da jam'iyya mai ci ta APC ta
mai she da ikirarin Atiku a matsayin bankaura da kuma hauragiya ta mafarki, ya
na ci gaba da dagiya kan samun nasara ta lallasa Buhari da tazara ta kimanin
kuri'u miliyan 1.6.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi