Wasu 'yan bangar siyasa wadanda ake
zargin magoya bayan jam’iyyar APC ne sun kai farmaki a gidan Babban Lauyan
Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Sakkwato Barista Sulaiman Usman
(SAN) a yammacin jiya tare da muzgunawa jama’a.
Da yake yi wa nanema labarai bayani
a Cibiyar Lauyoyi ta Gamzaki a Arkilla, Babban Lauyan Nijeriya, Barista
Sulaiman Usman ya bayyana cewar a lokacin da lamarin ya faru yana wajen yakin
neman zaben PDP a Karamar hukumar Kware.
A cewar sa 'yan bangar siyasar sun
yi aika-aikar ne da hadin bakin wasu jami'an 'yan sandan jihar da kuma wani dan
dabar da ake cewa Bashiru Marar-Guiwa.
Kwamishinan ya bayyana cewar wannan
ba shine karo na farko ba da hakan ke faruwa domin kuwa hakan ta faru a baya a
shekarar 2008 a filin jirgi zai je Abuja daga Sakkwato shekaru 10 da suka
gabata.
Daga karshe dai, kwamishinan yayi
kira ga Kwamishinan ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro a jihar da su dauki
matakin da ya kamata ta hanyar zakulo wadanda lamarin ya shafa tare da hukunta
su domin ya zama darasi.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi