Legit Hausa
Hukumar zabe mai zaman kan ta ta
kasa a tarayyar Najeriya watau Independent National Electoral Commission (INEC)
tace yanzu ta yanke shawarar ta sake gudanar da zabukan kujerun wasu 'yan
majalsun tarayya a jahohi 14 a fadin kasar.
Kamar dai yadda muka samu daga
hukumar, zabukan sun shafi na kujerun majalisaun dattawa guda bakwai da kuma na
'yan majalisun wakilai 24 a jahohin 14.
Legit.ng Hausa ta samu cewa shugaban
hukumar ta Independent National Electoral Commission (INEC), farfesa Mahmood
Yakubu ne ya bayyana wannan matsayar ta hukumar a garin Abuja yayin wani taron
masu ruwa da tsaki kan zabukan watau Inter-Agency Consultative Committee on
Elections Security (ICCES).
A cewar sa, hukumar ta dauki matakin
soke zabukan wasu rumfuna ne a yankunan lokacin zabukan da suka gabata sati
biyu da ya wuce sakamakon hargitsi, satar akwati da kuma wasu sauran
laifuffukan da suka jibinci zaben.
A wani labarin kuma, sashin dake
kula da manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan Najeriya dake Yaba, jihar Legas
ya fara gudanar da bincike bisa zargin cin hanci da ake yiwa DPO mai kula da
sashin Pen Cinema mai suma Harrison Nwabuisi.
Majiyarmu ta bayyana mana cewa, DPO
tare da wandasu jami’an ‘yan sanda ana zargin sune da amsar na goro daga wajen
mazauna unguwar Alimi Ogunyemi dake Ijeiye.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi