Legit Hausa
Rahoton da Legit.ng Hausa ta samu
daga jihar Jigawa sun nuna cewar an saki sakamakon karamar Babura, mahaifar
gwamnan jihar, Mohammed Abubakar Badaru.
Ga sakamakon kamar haka: Karamar
hukumar Babura Kujerar gwamna APC 43,601 PDP. 9,113 SDP. 1,184 Majalisar dokoki
APC 26,043 PDP 4,610 Karamar hukumar Kafin Hausa Gwamna APC: 38,989 PDP: 10,133
SDP: 7,725 Rahotanni daga jihar Sokoto sun nuna cewar an saki sakamakon karamar
Tambuwal, mahaifar gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal.
Ga sakamakon kamar haka: Aadadin ma
su kada kuri’a:123,749 Aadadin ma su kada kuri’a da aka tantance: 75,941
Kujerar gwamna APC: 29,081 PDP: 42,830 Majalisar dokoki APC: 15,328 PDP: 24,547
Zan rugumi kaddara idan na fadi zabe - Tambuwal Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya
ce zai rungumi kaddara ya amince da sakamakon zabe idan ya sha kaye.
A yayin da ya ke jawabi bayan kada
kuri'arsa, Tambuwal ya ce Allah ne ke bayar da shugbanci su kuma al'umma kawai
nasu fada ne. Kamar yadda aka sani, a yau Asabar 9 ga watan Maris ne Hukumar
Zabe Mai Zaman Kanta INEC ke gudanar da zabukkan gwamnoni da 'yan majalisun
jihohi a jihohi 29 na Najeriya.
Kamar yadda aka zaba, Legit.ng za ta
kasance tare da ku domin kawo muku abubuwan da ke wakana a jihohi inda a wannan
shafin za mu rika kawo muku yadda zaben ke tafiya a jihohin Sokoto, Jigawa da
Kebbi. Daga jihar Sokoto: Tsohon gwamna Aliyu Wamako ya kada kuri'arsa A halin
yanzu dai an fara kai kayayakin zabe zuwa rumfunan zabe kuma al'umma sun fito
domin kada kuri'arsu.
Manyan 'yan takarar gwamna a jihohin
sune: Jihar Sokoto 1. Ahmad Aliyu - Jam'iyyar APC 2. Aminu Tambuwal - Jam'iyyar
PDP Rahotannin da muka samu daga jihar Sokoto ya nuna cewa wasu 'yan daba sun
hana al'umma kada kuri'a a Magajin Gari da ke karamar hukumar Sokoto ta Arewa.
Jihar Jigawa 1. Muhammadu Badaru - Jam'iyyar APC 2. Aminu Ibrahim - Jam'iyyar
PDP 3. Bashir Adamu - Jam'iyyar SDP Rahotannin da muke samu a jihar Jigawa na
nuna cewa an fara gudanar da zabe a mafi yawancin rumfunan zabe da ke jihar
kuma na'urorin tantance kadin zabe wato Card reader suna aiki yadda ya kamata.
An kuma ruwaito cewa mai martaba
Sarkin Ringim, Dr Sayyadi Mahmoud Usman (CON) ya kada kuri'arsa a garin na
Ringim.
A halin yanzu mun samu rahoton cewa
gwamnan jihar Jigawa mai ci, Muhammadu Badaru ya kada kuri'arsa, ya kuma yi
kira ga al'umma su gudanar da zaben cikin zaman lafiya domin samun cigaban
jihar.
JIhar Kebbi 1. Abubakar Bagudu -
Jam'iyyar APC 2. Isa Galaudu - Jam'iyyar PDP A halin yanzu dai an kammala zabe
a mafi yawancin rufunnan zabe na jihohin Najeriya har ma an fara kirga kuri'un.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi