Kai-Tsaye: Yadda zaben gwamna na raba gardama ke gudana a jihar Sokoto


Legit Hausa

An fara kada kuri'a a rumfar zabe mai lamba 003 a mazabar Rafi B a karamar hukumar Sokoto misalin karfe 8.27 Zabe yana tafiya yadda ya kamata a karamar hukumar Sokoto ta Arewa Zabe yana tafiya lafiya kalau a Hubare 004 (PU), a karamar hukumar Sokoto ta Arewa inda aka fara jefa kuri'a misalin karfe 8 da rabi na safe.

An fara samun rashin jituwa a rumfar zabe Duk da cewa ba a fara kada kuri'a ba, an fara samun rashin jituwa tsakanin wakilan jam'iyyu a rumfar zabe mai lamba 12 (Sarkin, Adar, Atiku) inda jami'in zaben ya ce na'urar card reader da aka bashi bata aiki yadda ya kamata.

Bayan zaben gwamnoni da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris a jihohin Najeriya, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC ta bayyana cewa zabe bai kammalu a wasu jihohi shida ba, jihohin sun hada da Adamawa, Bauchi, Benue, Kano, Plateau and Sokoto. Hukumar ta dauki matakin ne saboda sashi na 34 (e) na dokokin zabe da ya ce zabe ba zai kammala ba idan tazarar kuri'un da ke tsakanin dan takarar da ya lashe zabe da mai biye masa ba su dara adadin kuri'un da aka soke ba.

Wannan dalilin ne yasa INEC ta zabi ranar 23 Maris domin gudanar da zaben raba gardama. A jihar Sokoto dai jam'iyyar PDP ce ke kan gaba da kuri'u 3,412 a zaben ranar 9 ga watan Maris. A yau kuma za a gudanar da zabe a mazabu 135 a kananan hukumomi 22 na jihar inda ake sa ran mutane 75,403 za su kada kuri'a.

A wannan shafin zamu rika kawo muku yadda zaben raba gardamar ke kasancewa a jihar Sokoto. A halin yanzu rahoton da muka samu daga Punch na nuna cewa an fara kada kuri'u a rumfar zabe mai lamba 004 da ke Rijia a jihar Sokoto.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN