Type Here to Get Search Results !

Main event

Yanzu: Kotu ta tabbatar da Adeleke na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Osun


Legit Hausa

Kotun da ke sauraron korafe korafen zaben gwamnan jihar Osun da ke da zama a babban birnnin tarayya Abuja ta bayyana jam'iyyar PDP da dan takararta a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a shekarar 2018, Sanata Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Kotun ta kuma yanke hukuncin cewa ba jam'iyyar APC da dan takararta, Gboyega Oyetola ba ne suka lashe zaben, don haka ta kwace nasarar da aka baiwa jam'iyyar bayan zaben jihar zagaye na biyu. Dan takarar jamiyar APC, Gboyega Oyetola ya doke abokin takarar sa na jamiyar adawa ta PDP, Ademola Adeleke, a zaben gwamnan jihar Osun da aka sake gudanarwa zagaye na biyu da tazarar kuri'u 483.

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta sanar da sakamakon zaben bayan karashen zaben da aka gudanar a wasu mazabu da aka dakatar da zaben su. Sai dai bayan sanar da sakamakon zaben, Sanata Adeleke da jam'iyyarsa ta PDP sun garzaya kotun sauraron korafe korafen zaben gwamnan, inda suka bayyana cewa ba su amince da sakamakon zaben ba.

 DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies