Legit Hausa
Wani babban jigon jam'iyyar All
Progressives Congress (APC) mai mulki, Farouk Adamu Aliyu ya bayyana cewa
jam'iyyarsu ta koyi darasi akan yadda aka gudanar da zabubbukan kasar na wannan
shekarar.
A wata hira da ya yi da shafin BBC
ya bayyana cewa rabuwar kan 'yan takara na daya daga cikin abubuwan da suka
kawo ma jam'iyyar cikas, har zama ta fuskanci kalubale a wasu jihohi wanda
hakan ya yi tasiri wajen rasa wasu kujerun gwamnoni da ma na 'yan majalisa.
Ya yi misali da jihar Ogun inda ya
bayyana cewa gwamnan ya yi ungulu da kan zabo inda gwamnan jihar dan APC ne
amma ya jagoranci wata jam'iyya domin ganin cewa an kada jam'iyyar APC a zaben
gwamna.
Ya yi kira ga jam'iyyar APC mai
mulki a kasar kan cewa a shekarar 2023 ta tabbatar an yi zaben fitar da gwani
na jam'iyyar sahihi kuma ingantacce a duk fadin kasar.
Farouk wanda ya kasance tsohon
shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, ya ja hankalin Shugaban kasa
Muhammadu Buhari akan cewa alúmman kasar sun nuna masa soyayya a duk jam'iyyar
da ya shiga, saboda haka ya zama wajibi ya tabbatar da cewa APC ta dore.
Daga karshe Farouk ya kara bayyana cewa
za su ci gaba da zawarcin wadanda suka sauya sheka daga jam'iyyar APC don ganin
cewa an dawo da su saboda tafiya tare.
A wani lamari na daban, Legit.ng ta
rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai zabi mukarraban
gwamnatinsa a wannan karon bisa la'akari da cancanta da kuma dai-daito.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi