Buhari ya fadi dalilinsa na yin sallar Juma'a a masallacin fadar shugaban kasa


Legit Hausa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi sallar Juma'a ne a masallacin fadar shugaban kasa a maimakon babban masallacin kasa na Abuja saboda kaucewa cinkoson fitarsa ke janyo wa al'umma.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya ce shugaban kasan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambaya da tawagar limamai da manyan malaman addinin musulunci daga jihohi Najeriya suka yi masa yayin da suka kai masa ziyara a ranar Juma'a.

Tawagar limaman karkashin jagorancin Farfesa Shehu Ahmad Galadanci sun kai ziyara gidan gwamnati ne domin su yiwa shugaban kasar murna nasarar da ya yi a zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 23 ga watan Fabrairu. Shugaban kasar ya ce:

"A kan batun bukatar da kuka gabatar na nema in rinka zuwa sallar Juma'a a masallacin kasa, Ina rokon ku da ku fahimta cewa na fara yin sallar Juma'a ne a masallacin fadar shugaban kasa saboda in rage wahalhalun al'umma ke shiga idan na fita.

"Kamar yadda kuka sani, duk lokacin da shugaban kasa zai fita dole sai an takaita zirga-zirga a wasu wurare tare da kafa shinge a hanyoyi wanda hakan na iya janyo matsi ga masallata da sauran al'umma.

" Shugaba Buhari ya gode wa malaman bisa addu'o'i da goyon bayan da suke bawa gwamnatinsa inda ya tabbatar musu ba zai yi kasa a gwiwa ba wurin magance kallubalen tsaro da kasar ke fama da ita .

 DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN