Legit Hausa
Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu
Sanusi II ya shirya taron addu'a na musamman a ranar Asabar domin taya Gwamna
Abdullahi Ganduje murnar lashe zabe da rokon Allah ya yi masa jagoranci a
mulkinsa karo na biyu.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan
bayan magoya bayan Ganduje sun cire hotunnan Sarki Sanusi da ke ciki da wajen
dakin taron nadin sarauta na Kano da ke gidan gwamnati sakamakon zargin sarkin
da marawa dan takarar jam'iyyar PDP baya.
Sai dai kwanaki kadan bayan cire
hotunan, Gwamna Ganduje ya bayar da umurnin a mayar da hotunan inda ya ce duk
da cewa Sarkin yana shiga harkokin siyasa, babu wani shirin tsige shi a yanzu.
Amma kuma sai gashi Sarkin ya shirya
taron addu'a na musamman a babban masallacin Kano domin taya Ganduje murnar
lashe zabe da fatan Allah ya yi masa jagora a mulkinsa karo na biyu kamar yadda
mai magana da yawun gwamnan, Abba Anwar ya sanar.
"Wadanda suka hallarci taron
sun hada da hakimai, limamai na Kano da masu nazarin ilimin addinin musulunci a
yayin da shi kuma Ganduje ya hallarci taron tare da wasu 'yan fadarsa, da masu
bashi shawara na musaman da sauransu.
"Sarki Sanusi ya dauki lokaci mai tsawo
yana bayyani a kan muhimmancin yafiya da afuwa a kan duk wani harka na gwamnati
da alaka tsakanin al'umma inda ya ce 'yan kora ne ke janyo rashin jituwa
tsakanin al'umma.
Ya ce dole mu rika addu'a Allah ya
kare mu daga sharrinsu Sarki Sanusi ya cigaba da cewa, "Ba laifi bane
mutum ya fadi ra'ayinsa a kan abubuwa da ke faruwa a tsakanin al'umma. Amma
abinda ke da muhimmanci shine bayan zabe, al'umma su hada kansu wuri guda su
goyi bayan wanda ya yi nasara."
"Ya zama dole mu hada hannu
wuri guda mu gina jihar Kano. Ya zama dole muyi aiki tukuru kuma muyi addu'a
domin samun cigaba a jihar mu da kasar mu baki daya. "Muna fata Allah ya
kiyaye mu daga sharin munafikai daga dukkan bangarori.
Za mu cigaba da addu'a samun zaman
lafiya a jihar mu. Ya kamata al'umma su fahimci abinda ya fi muhimmanci shine
suyi addua'a Allah ya taimaki shugabanin mu. Ya kuma basu masu shawara na gari.
" Ya kuma shawarci gwamna
Ganduje ya rika bincike a kan duk wani labari a aka kawo masa domin a wasu
lokutan mutane na iya kirkirar labari domin su haifar da rashin jituwa tsakanin
al'umma.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi