Legit Hausa
Akwai kwararan alamu da ke nuna
cewar jam’iyyar APC mai mulki na son mayar da kujerar shugaban majalisaar
dattijai zuwa arewa sannan ta mika kujerar shugaban majalisar wakilai zuwa
yankin kudu. Yanzu haka jam’iyyar APC ke da ma fi rinjayen mambobi a majalisar
dattijai da ta wakilai. APC na da sanatoci 64 da mambobin majalisar wakilai
fiye da 200.
Wasu ma su ruwa da tsaki a tafiyar
da harkokin jam’iyyar APC na kulle-kullen ganin an mika kujerar shugaban
majalisar dattijai zuwa yankin arewa, musamman yankin arewa maso gabas, sannan
a bawa yankin kudu, musamman kudu maso yamma, kujerar shugaban majalisar
wakilai.
Legit.ng ta fahimci cewar ma su ruwa
da tsakin na son a bawa yankin kudu maso kudu kujerar mataimakin shugaban
majalisar dattijai, sannan a bawa yankin arewa maso ko arewa ta tsakiya kujerar
mataimakin shugaban majalisar wakilai.
Tuni sanatoci uku daga yankin arewa
maso gabas; Sanata Ahmed Lawan (Yobe), Sanata Ali Ndume (Borno), Sanata Danjuma
Goje (Gombe), da sanata daya daga yankin arewa ta tsakiya; Sanata Abdullahi
Adamu (Nasarawa), sun fara yakin neman zama shugaban majalisar dattijai.
A bangaren majalisar wakilai, Femi
Gbajabiamila (Lagos), Mohammed Tahir Monguno (Borno), da Abdulrazak Namdas
(Adamawa) sun nuna sha’awar yin takarar neman jagorantar majalisar wakilai.
Wasu mambobin da su ka nuna sha’awar
shugabancin majalisar wakilai su ne; Ahmed Idris Wase (Filato), Umar Bago
(Neja), da Babangida Ibrahim (Katsina). Abdulaziz Yari, gwamnan jihar Zamfara
mai baring ado, ya nuna sha’awar sa ta son zama mataimakin shugaban majalisar
dattijai.
Kazalika, ‘yan majalisar wakilai
biyu daga jihar Kano; Abdulrahman Kawu Sumaila da Aminu Suleiman Goro, sun nuna
sha’awar yin takarar kujerar mataimakin shugaban majalisar wakilai. Tuni
Gbajabiamila da Kawu sun fara tuntubar mambobin majalisar domin neman goyon
bayan su.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi