Type Here to Get Search Results !

Main event

Zargi: Yansanda sun kashe wani hafkan NSCDC da duka a Abuja

Wasu yansanda sun yi ma wani hafsan NSCDC mai tauraro 2 duka har ya mutu ranar Laraba da safe a Nyanya da ke babban birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun ce hafsan rundunar NSCDC  Ogar Jombo yana sanye da Kakinsa na aiki, ya dauko yaransa tare da matasa a cikin motarsa domin ya kai su makaranta, amma sai ya juya a wajen da bai kamata ba.

Ganin haka ke da wuya kamar yadda wani ganau ba jiyau ba ya shaida ma yan jarida, bayan yansanda sun tare shi ya nemi gafara tare da ba yansandan uzuri na kokarin ya kai yaransa makaranta, amma daga bisani sai suka kama dukansa kuma suka yi ta kwada masa kulki, lamari da ya zama ajalinsa daga karshe.

Tuni dai aka kama yansanda da suka aikata wannan danyen aiki kuma za su fuskanci hukunci, kamar yadda wani babban hafsan dansanda ya yi bayani.DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies