Type Here to Get Search Results !

An yi zina da ma'aikatan mu lokacin zaben shugaban kasa - INEC


Legit Hausa

Hukumar shirya zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commisslon (INEC) ta bada labarin cewa an yi zina da wasu ma'aikatan ta mata a yayin zabukan da aka gudanar satin da ya gabata na shugaban kasa da 'yan majalisar wakilai.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da babban jami'in yada labarai da wayar da kan masu zabe na hukumar Mista Festus Okoye ya fitar dauke da sa hannun sa A cikin sanarwar, Mista Festus Okoye ya bayyana cewa duk da dai zaben da aka gudanar a iya cewa an yi shi ne cikin lumana a dukkan fadin kasar, amma dai hukumar ta dan samu tsaiko a wasu wuraren yayin zaben.

Ya ciga da cewa hukumar ta Independent National Electoral Commisslon (INEC) ta samu labarin tashe-tashen hankula da satar mutane da yiwa jami'an su fyade da ma rasa rai a wasu wuraren. Haka zalika Mista Festus ya kuma yi anfani da damar wajen jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukan su ko jikkata koma rasa dukiya a wasu wuraren tare da basu hakuri da kuma tabbacin karin matakan tsaro daga hukumar domin kaucewa kara aukuwar lamarin a gaba
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN