Rahotanni masu karo da juna sun ce an kama mataimakin kakakin majalisar dokoki na jihar Nassarawa Hon Akwashiki na jam'iyar APC mai wakiltar Eggon na Arewa bayan ya yi kokarin aikata zina da wata matar aure a wani gida da ke unguwar Maitama a birnin Abuja ranar Juma'a da dare.
Matar da aka ce ya yi kokarin yin zina da ita matar wani dan siyasa ne mai suna Alh. Danladi Halilu Envuluanza(aka C.R) wanda jigo ne a jam'iyar ta APC a jihar Nassarawa.
Wata majiya ta ce dan siyasan ya dade yana neman wannan mata, amma sia ta dana masa tarko yadda za'a kama shi. Hon Akwashiki shi ne wanda ya lashe zaben kujerar Sanata mai wakiltar yankinsu a zabe da ya gabata.
Sai dai a wata sanarwa da ta fito daga bangaren Hon. Akwashiki, ya ce, ita wannan mata da ake zance tare da wasu mutane sun gayyaci Hon Akwashiki domin ya je gidan su taya shi murnar lashe zabe na kujerar Sanata da liyafar cin abincin dare.
Amma isarsa ke da wuya sai wasu yan daban siyasa suka afka masa da duka da zagi, suka yayyaga masa tufafi kuma suka tube shi suka yi ta daukan hotunansa suna wulakanta shi.
Bayanan sun kara da cewa sakamakon haka Akwashiki ya suma.Wani makwabcin gidan da lamarin ya faru kuma ganau ba jiyau ba ya shaida haka, daga bisani suka kai Hon. Akwashiki wani Asibiti domin samun kulawa.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi