Hukumar yansandan Najeriya ta kama wadanda suka kisa yadda aka kama kuma aka wulakanta wani mataimakin kwamishinan yansanda DCP Kola Okunlola a garin Twon-Brass da ke jihar Bayelsa ranar 24 ga watan Fabrairu.
Kakakin hukumar yansanda ACP Frank Mba ya ce an kama madugun batagarin wanda shi ne ya jagoranci wasu 'yan iska da suka wulakanta tare da cin zarafin mataimakin kwamishinan yansandan.
Shi dai wannan madugu wanda kuma dan takaran kujeran Majalisar dokoki na jihar Bayelsa ne Hon Israel Sunny Gioli ya fada hannun yansanda yau a birnin Abuja bayan ya tsere daga jihar Beyelsa bayan sun aikata wannan aika aika.
Sauran yaran nasa da yansanda suka kama sun hada da Tamarapreye Victor da Azi Newton dukansu masu shekara 34.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi