A jiya Laraba ne dai
kasashen Pakistan da Indiya suka mayarwa da juna martani ta hanyar
jijjigo jiragen juna bayan harin makonnin baya-bayan nan da ya hallaka
sojin Indiya da dama
Kasashen Pakistan da Indiya sun yi ikirarin kakkabo jiragen yakin juna, a
wani rikici da ke da da kamari tsakaninsu, kuma ake fargabar cewa za a
samu fito na fito tsakanin kasashen makwabtan juna masu makaman
nukiliya. Kasashen biyu dai na kai ruwa rana ne kan yankin Kashmir da ke
karkashin ikon Indiya, lamarin da ya yi sanadiyar hassala rikicin da ke
tsakaninsu a karon farko cikin shekaru 20.
Kakakin ma’aikatar tsaron Indiya, Raveesh Kumar, a yau Laraba ya ce an
fara zube-ban kwarya ne, bayan da sojin Pakistan suka fara kai hari kan
sojin da Indiya ta girke a yankin Kashmir.
A bangare guda Firaministan Pakistan, Imran Khan wanda ya nemi kasashen
biyu su tattauna don samar da mafita, ya ce duk da haka Pakistan ba za
ta tsaya ta na kallo ba, don kuwa za ta dauki matakan da suka dace don
kare kanta.
Firaminista Imran Khan ya kuma bayyana yadda jiragen yakin Indiya suka
ratsa kasarsa ba tare da izini ba, matakin da ya tilasta su kakkabo
jiragen tare da kame matukansu.
Rikicin ya tashi ne bayan wani harin bam da ya yi sanadin mutuwar
dakarun Indiya 40 a yankin Kashmir ranar 14 ga watan Fabarairu, hari
mafi muni cikin shekaru 30 na rikicin tsakanin India da Pakistan.
Read More at: https://hausa.leadership.ng/2019/02/28/an-buga-gangar-yaki-tsakanin-kasashen-pakistan-da-indiya/
Leadership HausaRead More at: https://hausa.leadership.ng/2019/02/28/an-buga-gangar-yaki-tsakanin-kasashen-pakistan-da-indiya/
A jiya Laraba ne dai kasashen
Pakistan da Indiya suka mayarwa da juna martani ta hanyar jijjigo jiragen juna
bayan harin makonnin baya-bayan nan da ya hallaka sojin Indiya da dama Kasashen
Pakistan da Indiya sun yi ikirarin kakkabo jiragen yakin juna, a wani rikici da
ke da da kamari tsakaninsu, kuma ake fargabar cewa za a samu fito na fito
tsakanin kasashen makwabtan juna masu makaman nukiliya.
Kasashen biyu dai na kai ruwa rana
ne kan yankin Kashmir da ke karkashin ikon Indiya, lamarin da ya yi sanadiyar hassala
rikicin da ke tsakaninsu a karon farko cikin shekaru 20. Kakakin ma’aikatar
tsaron Indiya, Raveesh Kumar, a yau Laraba ya ce an fara zube-ban kwarya ne,
bayan da sojin Pakistan suka fara kai hari kan sojin da Indiya ta girke a
yankin Kashmir.
A bangare guda Firaministan
Pakistan, Imran Khan wanda ya nemi kasashen biyu su tattauna don samar da
mafita, ya ce duk da haka Pakistan ba za ta tsaya ta na kallo ba, don kuwa za
ta dauki matakan da suka dace don kare kanta.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi