Type Here to Get Search Results !

2019: Ganduje ya sha kashi a hannun PDP a Unguwar Magwan


Legit Hausa

Mun samu labari cewa kam’iyyar PDP mai adawa a jihar Kano ce ta lashe akwatin Unguwar Magwan inda nan ne mataimakin gwamnan jihar Kano watau Dr. Nasiru Yusuf Gawuna yake zabe.

 ‘Dan takarar PDP, Abba Kabir Yusuf, shi ne yayi nasara a rumfar zaben da ke Magwan da ke cikin Unguwar Gawuna a cikin karamar hukumar Nasarawa.

Abba Yusuf ya lashe duka akwatuna 3 da ke cikin Magwan a zaben yau. Daily Trust ta rahoto PDP ta samu kuri’a 210 ne a yankin yayin da APC mai mulki ta samu kuri’u 197. Har a akwatin da mai girma mataimakin gwamna yake yin zabe, ‘dan takarar PDP Abba Yusuf ya doke APC da kuri’a 3.

Jaridar tace jam’iyyar PDP ta samu kuri’a 76 inda APC kuma ta tashi da 73 a rumfar Nasiru Gawuna da ke cikin Magwan. A sauran akwatun yankin, PDP mai adawa ta samu 63 da 76 yayin da APC ta iya samun kuri’u 48 da kuma 71.

A yau dinne kuma aka damke wata mota cike makil da kayan zabe a wata makaranta da ke cikin Magwan din inda nan ne Yankin da Mataimakin Gwamnan jihar Kano Nasiru Gawuna mai-ci ya fito.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN