Type Here to Get Search Results !

Ana cigaba da kirga kuri'un zaben Gwamna da 'Yan Majalisa a Kano


Legit Hausa

Ga dai wasu daga cikin rahotannin da mu ke samu daga wasu akwatuna a jihar ta Kano.

 Tattarawa Ward, Dawakin Tofa PU 004 Majalisa PDP 48 APC 238 Rejected 0 Gwamna PDP 53 APC 231 Rejected 3 Tattarawa Ward, Dawakin Tofa Majalisa PDP 50 APC 171 Rejected 13 Gwamna PDP 58 APC 162 Gumduma Tudun Wada B PU 07 Akwatin Gwamna APC 84 PDP 18 Majalisa APC 84 PDP 19 Gurjiya Ward Dawakin Kudu PU 008 Zaben Gwamna APC 147 PDP 94 Unguwar Yanganau, Tsanyawa. PU 004 Sallawa Takatsaba Zaben Gwamna APC= 181 PDP= 152 PRP= 011 Gurun Ward, Tsanyawa PU 005 D/mahuta Zaben Gwamna APC-110 PDP-41 PRP-0 Majalisa APC-110 PDP-42 PRP-1 Sai dai har yanzu hukumar INEC ba ta tabbatar da wadannan sakamako ba tukuna. KU KARANTA: An kai hari a wani Gari a Kaduna ana shirin zaben Gwamna Nariya a karamar hukumar Kibiya Gwamna PU 007 PDP 141 APC 86 Invalid 4 Majalisa PDP 137 APC 84 Invalid 8 Gandun Albasa a Karamar hukumar Birnin Kano Akwatin makarantar Firamare APC 27 PDP55 PRP14 Majalisar dokoki APC* -40 PDP* -50 PRP* -3

 Tuni dai gwamna Abdullahi Ganduje da Mai dakin sa watau Hajiya Dr. Hafsat Umar Ganduje su ka kada kuri’ar su a zaben na yau.

Haka shi ma ‘Dan takarar jam’iyyar PRP, Salihu Takai ya kada ta sa kuri’ar a mazabar sa. Kamar yadda mu ka ji an samu takaddama a yankin Mandawari inda magoya bayan ‘dan takarar PDP watau Abba Kabir Yusuf su ka hadu da Mabiyan APC da ke tare da shugaban jam’iyya na jihar watau Abbas Sanusi.

Kwamishin ‘yan sanda na jihar Kano watau Muhammad Wakili ya kawo ziyarar ba-zata zuwa Yankin na Mandawari da ke cikin birnin Kano domin ganin an yi zabe lafiya. Akwai dai manyan ‘yan siyasan Kano a yankin.

Haka kuma mun ji cewa dazu nan Jami’an tsaro su kayi nasarar damke wata mota cike makil da kayan zabe a wata makaranta da ke Magwan da ke cikin Yankin Gawuna inda Mataimakin Gwamnan jihar Kano mai-ci ya fito.

Ana kukan cewa ana amfani da kudi wajen sayen kuri’un jama’a yayin da a wasu wurare kuma ake kukan cewa ba a kai isassun kayan zaben da ake bukata ba kamar yadda mu ke samun labari.

 DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN