Rundunar yansandan jihar Lagos ta ceto wasu yara kanana yan makarantar Framare su 12 da aka shigar da su wata kungiyar asiri.
Rahotannni sun ce wata yarinya mai suna Rasheedat mai shekara 16 wacce ke karatu a babban makarantar sakandare na Grammer da ke Igando ce ta shigar da yaran kungiyar asiri da ake kira Awawa.
Wani malami ne ya kula da wata alama a gefen gemun wasu yara, wanda sakamakon haka ya yi bincike da ya sa wani yaro ya fallasa cewa duk yaro da aka gani da wannan alama yana cikin kungiyar asiri mai suna Awawa.
Yansanda na ci gaba da bincike kan lamarin, kuma har an kama wasu samari guda 2 suna taimaka ma yansanda a bincike.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi