Legit Hausa
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ce Allah ne
kadai zai iya yiwa barayin 'yan jam'iyyar adawa ta Peoplees Democratic Party
(PDP) da suka tafka sata ta tashin hankali lokacin da suke kan madafun iko
hisabi.
Shugaban kasar dai yayi wannan kalaman ne lokacin da yake
labartawa wasu mambobin kunyoyin dake goyon bayan tazarcen sa irin cikin halin
takaicin da ya tsinci kasar a shekarar 2015 bayan lashe zaben sa.
Legit.ng Hausa ta tsinkayi cewa shugaban kasar wanda ya rika
magana cikin takaici ya bayyana cewa jam'iyyar ta adawa ta Peoplees Democratic
Party (PDP) ba karamar ta'asa ta tafka ba a tsawon shekaru 16 da ta yi tana
mulkar Najeriya. Ya kara cewa duk da yake idan aka kiyasta, jam'iyyar ta rika
sayar da gangar danyen mai akan farashin $100 ne a lokacin mulkin ta, jam'iyyar
bata tsinanawa kasa komai ba tsawon lokacin sai ma dai satar da suka yi ta yi
ba kama hannun yaro.
Daga karshe sai shugaban kasar yace shi ba abun da zai ce da
'yan PDP din sai Allah ya isa domin shine kadai zai iya sakawa 'yan Najeriya
cutar su da jam'iyyar ta Peoplees Democratic Party (PDP) tayi.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi