Wani Dansanda Ya Kashe Dan Acaba Da Bindiga Saboda Siyasa


Legit Hausa

Rahotanni sun bayyana cewa wani dan acaba ya gamu da ajalisan a lokacin da wani dan sanda a jihar Ondo ya harbe shi har lahira

Dan sandan, yana aiki ne a cikin masu tsaron lafiyar wani dan majalisar wakilan tarayya karkashin jam'iyyar SDP da ke wakiltar mazabar Idanre/Ifedore

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda na jihar Mr Femi Joseph, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce zai yi cikakken bayani nan ba da jimawa ba Rahotanni sun bayyana cewa wani dan acaba wanda har yanzu ba a bayyana ko wanene ba, ya gamu da ajalisan a lokacin da wani dan sanda a garin Ipogun, karamar hukumar Ifedore da ke jihar Ondo ya harbe shi har lahira a ranar Alhamis.

Dan sandan, wanda shima har yanzu ba a bayyana sunansa ba, yana aiki ne a cikin masu tsaron lafiyar wani dan majalisar wakilan tarayya karkashin jam'iyyar SDP da ke wakiltar mazabar Idanre/Ifedore a majalisar tarayya, mai suna Tajudeen Adefisoye.

A cewar rahotannin, dan takarar ya fita yakin zabensa na da misalin karfe 6:30 na yamma a lokacin da lamarin ya faru. Legit.ng Hausa ta samu rahoton cewa dan takarar ya isa garin Ipogun domin yakin zabensa, inda dandazon masu acaba suka dumfare shi.

A haka ne wani dan sanda da ke tsaron lafiyar dan majalisar ya harbi daya daga cikin 'yan acabar a goshinsa, wanda ya mutu nan take. Wannan lamari dai ya haddasa barkewar zanga zanga daga abokan aikin wanda aka kashen, inda har suka so gfarwa dan majalalisar, wanda ya sha da kyar tare da tserewa daga wajen.

Rahotanni sun bayyana cewa matasan da suka harzuka, sun kona motocin yakin zaben dan majalisar guda biyu. Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda na jihar Mr Femi Joseph, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce zai yi cikakken bayani nan ba da jimawa ba.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN