Yan isks sun hargitsa taron PDP a Lagos har da jifar junansu da kujeru

Legit Hausa

Wasu yan iska sunyi yunkurin hargitsa yakin neman zabe da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ke gudanarwa a filin Tafawa Balewa (TBS) da ke jihar Lagas.

Rikici ya barke ne tsakanin wasu matasa kusa da aihanin munbarin da shuwagabanin jam’iyya ke zaune.

Lamarin, Wanda ya faru misalin karfe 1:50 na Rana, ya hada da jefe jefen kujeru da kuma fadace-fadace.

Ba a gano mussababin faruwa rikcin ba. Wadanda ke a haraban sun tsere, yayinda yan sanda suka kore yan iskan daga wajen.

Yanzu Yanzu: Rikici ya barke a gangamin PDP a Lagas inda yan daba ke ta jifan junansu da kujeru
Yanzu Yanzu: Rikici ya barke a gangamin PDP a Lagas inda yan daba ke ta jifan junansu da kujeru

Lamarin ya fara ne a lokacinda aka soma mikawa yan takaran mukaman majalisa tutar jam’iyya.

A cewar mai gabatarwa: “naga alamun wassu sun zo nan ne don tayar da hankali. Za a hukunta Wadanda suka zo nan don tada hankali a matsayin masu laifi.”

An chaje kowa kafin shiga cikin filin wasan gabannin fara shirin. Haka zalika, an hango wasu matasa na shan ganye a haraban, yayinda aka baiwa masu siyar da Kayan ruwa izinin siyar da kayan maye.

Ana kyautata zaton cewa dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar zai gabatar da jawabai nan da yan guntun lokaci.


Ku biyo cikin shafukan mu na zaur
Previous Post Next Post