Atiku ya sake ssmun yan takarar shugaban kasa 2 da suka goyi bayansa

Legit Hausa

Kasa da kwanaki hudu zaben shugaban kasa, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Coalition Party (PCP) Dr. Nicolas Felix tare da takwaransa na jam'iyyar All Grass Alliance (AGA) Chuks Nwachukwu, sun janye daga takararsu tare da goyon bayan dan takarar jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar.

A wani bukin siyasa da ake kan gudanarwa a Abuja, 'yan takarar shugabancin kasar guda biyu sun yi kira ga daukacin magoya bayansu da su goyi bayan Atiku tare da kada masa kuri'unsu a zaben ranar Asabar mai zuwa.

Sun bayyana cewa dan takarar shugaban kasar karkashin jam'iyyar PDP yana da karfin iko da basirar samar dora kasar a turba ta ci gaba, haka zalika sun zabi goyon bayansa domin yakinin cewa ba zai tafi ya barsu a baya ba idan har ya samu nasara.


Cikakken labarin yana zuwa...

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN