Buhari ya gudanar da yakin neman zabe a Abuja (Hotuna)

A yau Laraba, 13 ga watan Fabrairu, shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyya mai ci ta APC, ya gudanar da taron sa na yakin neman zabe cikin babban birnin kasar nan na tarayya Abuja.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya nufaci babban filin taron kasar nan na Eagle Square da ke garin Abuja bayan halartar taron rattaba hannu kan yarjejeniyar aminci da tabbatar da zaman lafiya gabani da kuma bayan babban zabe.
A yayin da a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu, za a gudanar da babban zabe na kasar nan, a yau kuma shugaba Buhari da dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar amincewa da duk yadda sakamakon zaben zai kasance.

Baya ga amincewa da sakamakon zabe, kazalika yarjejeniyar ta hadar ta shan alwashi na tabbatar da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali gami da lumana gabani da kuma bayan zabe tsakanin manyan 'yan takarar biyu.
Cikin wani rahoto mai nasaba da wannan, a yau ne jam'iyyar PDP ta shirya gudanar da taron ta na yakin zaben kujerar shugaban kasa cikin garin Abuja, inda daga bisani ta janye tare da daukar dangana sakamakon yadda jam'iyya mai ci ta APC ta yi ma ta kaka-gida.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN