Kebbi: Yadda aka farfado da gidan Radiyon Zuru domin neman biyan bukatar siyasa | ISYAKU.COM

Tun zamanin mulkin tsohon Gwamnan jihar Kebbi Adamu Aliero, zamani da aka yi amfani da nuna karfin mulki da jama'ar kasar Zuru suke wa fassarar "danniya da zalunci", lokaci da aka dauke na'urar watsa labarai na gidan rediyon Zuru aka mayar garin Birnin kebbi, alhali ba wai Gwamnatin waccan zamani ta rasa kudin sayen na'urar watsa labarai wanda aka bari ya lalace bane a gidan rediyon Kebbi Radio dake Birnin kebbi.

Wani abin mamaki shi ne, bayan kusan shekara 20, gwamnatocin jihar Kebbi karkashin jagorancin Gwamnoni da suka shude suka ki wadatar da gidan rediyo da gangan ga al'ummar kasar Zuru. Sai a wannan lokaci  Gwamna Atiku Bagudu ya sa aka yi ma gidan rediyon kwaskwarima domin neman biyan bukatarsa ta siyasa.

Dan Bagudu ya karbi mulkin jihar Kebbi a watan Mayu na 2015 tare da mataimakinsa Samaila Yombe, wanda 'dan kasar Zuru ne, amma sai a daidai wannan lokaci na yakin neman a sake zabarsu ne suka tuna da zancen gidan rediyon Zuru wanda a yanzu haka idan bancin cika masu sauraro da wakokin siyasa na goyon bayan Gwamna Bagudu babu wani abin da wannan rediyo ke watsawa.

A gefe daya kuma. akwai zancen cewa gwamnatin 'dan Bagudu ta wadatar da kasar Zuru da wuntan lantarki domin an raba wutar Zuru da ta Yauri. Ammafa Zuru ta 'dandana bakar wulakanci na rashin kulawar shugabanni masu mulkin jihar Kebbi karkashin jagorancin Gwamnoni 'yan asalin Hausa ko Fulani, sai a wannan lokaci da 'Dan Bagudu ke neman kuri'un mutanen kasar Zuru.

Wani babban lamari kuma shi ne yadda Gwamna Bagudu ya kasa tabbatar da Mai shari'a Justice Asabe Karatu, wacce Gwamna Bagudu ya ki tabbatar da ita a matsayin babban Jojin jihar Kebbi wanda jama'ar kasar Zuru musamman Kiristoci ke wa kallon yanayi na nuna banbancin addini ko kabilanci domin asalinta na kasancewa Badakkara 'yar asalin kasar Zuru kuma Kirista.

ISYAKU.COM ya tattaro cewa Gwamna Bagudu ya shiga har cikin Chochi a kasar Zuru domin neman kuri'ar al'umman Kiristoci na kasar Zuru. Amma fa bincike da muka gudanar ya tabbatar cewa akwai al'umman Kirista da yawan gaske da ke neman saka wa Kura da aniyarta ta akwatin zabe. Domin dai suna matukar mutunta Mai shari'a Justice Asabe Karatu da tsarin Gwamnatin jihar Kebbi ta ki kaddamar da ita a matsayin babban Jojin jihar Kebbi duk da yake Majalisar kula da harkokin shari'a na kasa National Judicial Council NJC ta amince da Justice Asabe Karatu a matsayin babban Jojin jihar Kebbi, amma Gwamnan jihar Kebbi ya ki rantsar da ita.

Idan baku manta ba, Majalisar Dokoki na jihar Kebbi ta ce akwai gyara a takardun framare na Justice Asabe Karatu, wai shi ne dalili da ya sa basu wanke ta ba balle Gwamnatin jihar Kebbi ta rantsar da ita. Amma tuni Justice Asabe ta nisanta kanta da wannan zargi wanda masu fashin baki ke wa fassarar neman ganin laifi da karfi da yaji , wata muguwar tabi'a da ta dade tana hana jihar Kebbi ci gaba domin mugun nufi da neman hana ruwa gudu daga wasu kalilan jama'a da mutuncinsu ya ta'allaka ne  kawai ga biyan bukatar kansu. Domin dai da wannan takardu Justice Asabe Karatu ta yi karance karancenta har zuwa wannan lokaci fiye da shekara 34, sai yanzu a Majalisar Dokoki na jihar Kebbi ne aka fi kowa iya bincike da aka gano takardun faramare ba na sakandare ko jami'a ba akwai gyara.

Duk da yake Majalisar Dokoki na jihar Kebbi tana gudanar da aikinta ne tare da zubin irin mutane da ta sami kanta a halin yanzu, da kuma bukatu irin na shugabancin jihar Kebbi. Amma tabbas ne cewa ko wa jima ko wa dade, abin da aka aikata ma Justice Asabe Karatu zai zama shaida da hujja a kan duk wanda ke da hannu a kan abin da aka aikata mata, kuma tarihi zai maimaita kanshi kan wadanda ke da hannu. Hakazalika amana da tarihi ba zai taba yafe masu ba.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN