Muna zargin hukumar INEC tana yi wa PDP aiki - Oshiomhole

Leadership Hausa

Ciyaman din jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya wato Adams Oshiomhole, ya zargi hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC da cewa tana yiwa jam'iyyar adawa ta PDP aiki ne.

Adams Oshiomhole, ya bayyanawa manema labarai hakan ne a yau Laraba a birnin tarayya Abuja, inda ya ce; hana jam'iyyar ayyana dan takara a jihohin Ribas da Zamfara da hukumar INEC din ta yi, ya sa su sanya alamar tambaya akan hukumar ta INEC din, kuma hakan ya sanya su damuwa. Ya kara da cewa; "INEC ba ta yiwa APC adalci ba.

Hukumar kamar tana yiwa PDP aiki ne." Inji Oshiomole. Karin bayani na nan tafe……..  

0/Post a Comment/Comments

Rubuta ra ayin ka

Previous Post Next Post