Zabe: Sakamako daga jihohin Sokoto, Kebbi da Jigawa


Legit Hausa

A jiya, Asabar, 23 ga watan Fabarairu ne aka gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majlisar tayya ('yan majalisar wakilai da dattijai) a fadin kasar nan.

Tun a jiyan sakamako su ka fara fitowa daga mazabu daban-daban da ke fadin kasar nan. Sai dai har yanzu hukumar zabe ta kasa (INEC) ba ta fara fitar da sakamako a hukumance ba.

Zaben dai ya fi jan hankali ne a matakin kujerar shugaban kasa tsakanin manyn ‘yan takara; shugaba Buhari a jam’iyyar APC da babban abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar PDP. Manema labarai da ‘yan jarida sun fi mayar da hankali a kan sakamakon mazabun manyan ‘yan siyasa da ke goyon bayan ‘yan takarar biyu.

A yayin da aka kammala kad'a kuri'u a wasu sassa na jihohi 36 na kasar Nigeria, ciki kuwa har da jihohin Sokoto, Jigawa da Kebbi, tuni aka fara tattara kuri'u tare da kidaya su a wasu rumfunan zabe na jihohin.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN