Type Here to Get Search Results !

Kai tsaye: Sakamakon zabe daga jihohin Niger, Kwara da Nasarawa


Legit Hausa


An dai gudanar da zabe cikin lumana da kwanciyar hankali a wadannan jihohi guda uku na kasar. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne kan gaba a yanzu haka yayinda INEC ke ci gaba da hada sakamakon zabe na jihar Kwara, APC na da 11,051 inda PDP ke da 4,904 daga karamar hukumar Oyun.

 Hakazalika APC na da 6,079 yayinda PDP ke da 6,242 a karamar hukumar Oke-Ero. Sannan APC na da 6,662 yayinda PDP ke da 5,397 a karamar hukumar Ekiti. A Asa, APC na da 15,976, yayinda PDP ta samu 10,705. A Irepodun, APC na da 14,395, PDP na da 10,232. A Karamar hukumar Mooro na da APC scored 17,534 sannan PDP na da 7,598.

A Ilorin East, APC ta tashi da kuri’u 31,039 sannan PDP ta samu 12,820. Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya fadi a daya daga cikin kananan hukumomi hudu a yankin Kwara ta tsakiya a zaben majalisar dokokin kasar da aka gudanar a ranar Asabar. Mista Saraki dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya sha kaye a hannun Ibrahim Oloriegbe na APC. Akwai kananan hukumomi hudu a yankin wanda suka hada da Asa, Ilorin West, Ilorin East da kuma Ilorin South.

Yayinda hukumar zabe ke sanar da sakamako a ofishin INEC a ranar Lahadi a karamar hukumar Asa, Mista Saraki na ya samu kuri’u 11, 252, yayinda dan takarar APC ya samu 15,932.

Jami’in zabe ya bayar da adadin masu rijista a matsayin 73,425, yayinda aka tantance masu zabe 29,023. Kwara: Ilorin east LGA, Kwara central Senatorial election result Oloriegbe (APC): 30014 Bukola saraki (PDP): 14654 A halin da ake ciki, Dan takarar APC na gaba da Saraki da kuri’u 20,000 a biyu daga cikin kananan hukumomi hudu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasance tare damu yayinda muke ci gaba da tattaro maku sakamakon zabukan da suka gudana a fadin kasar a yau A karamar hukumar Bida da ke jihar Niger Zaben Shugaban kasa APC: 40050 PDP: 5749 Azara Ward, jihar Nasarawa Shugaban kasa APC:4360 PDP: 2036 Agawada Ward, jihar Nasarawa Shugaban kasa APC: 3234 PDP: 2340 Kofar Gwari Ward, jihar Nasarawa Shugaban kasa APC: 1852 PDP: 1838 Ninkoro Ward, Nasarawa Shugaban kasa APC: 3610 PDP: 3738 Mazabar 009; Kere Aje. Karamar hukumar Offa, Jihar Kwara. Zaben shugaban kasa APC - 116 PDP - 23 A yankin mazabar OO2 ward 4 Ikole shugaban kasa Buhari na gaba da Atiku Zaben shugaban kasa: APC 81 PDP 24 Zaben Sanata: APC 83 PDP 27 Zaben yan majalisar wakilai: APC 87 PDP 27 PU 011, Iludun Oro, Irepodun LGA, Kwara south Shugaban kasa: APC 55 PDP 24 PCp 1 Invalid 1 Majalisar dattawa APC 48 PDP 32 PPN 1 Majalisar wakilai: APC 54 PDP 21 ADC 4 Accord 1 PT 1 PPN 1 PU 003, Oro, Irepodun LGA, Kwara South Shugaban kasa: APC 191 PDP 86 ADC 2 PCP 2 NCP 1 ACD 1 ACPN 1 APDA 1 Majalisar dattawa: APC 197 PDP 78 ADC 6 LP 1 ADP 1 PDC 1 Majalisar wakilai: APC 196 PDP 81 PDC 1 ADC 12 PU 009; Kere Aje Ward, Offa LGA, Kwara South Shugaban kasa: APC 116 PDP 23 Majalisar dattawa APC 122 PDP 22 Majalisar wakilai: APC 112 PDP 22 PU 01, Okerimi Oro, Irepodun LGA, Kwara South Shugaban kasa: APC 98 PDP 72 Majalisar dattawa: APC 90 PDP 78 Majalisar wakilai APC 87 PDP 85 PU 002; Essa B Ward, Offa LGA, Kwara South Shugaban kasa APC 341 PDP 76 Majalisar dattawa ANP 3 APC 340 PDP 72 Majalisar wakilai APC 330 PDP 83 PU 003; Shawo South/East Ward, Offa LG, Kwara State Shugaban kasa: AA 0 APA 02 APC 261 ANP 03 PCP 01 PDP 46 NCP 0 UPN Majalisar dattawa: APC 269 ANP 2 PDP 45 Majalisar wakilai: AA 1 APC 252 ANP 4 PDP 56 NCP 1 UPN 1 PU-8, Asa LG, Kwara State Shugaban kasa: APC - 59 PDP- 36 Majalisar dattawa: PDP- 34 APC- 67 PDC- 2 Majalisar wakilai: APC: 63 PDP: 37 PU004 Balogun Alanamu ward 5 of Ilorin West LG in Kwara Central. Shugaban kasa: APC: 50 PDP: 044 ADC:001 Majalisar dattawa: APC: 043 PDP: 049 Majalisar wakilai APC:046 PDP: 048 ADC: 001 PU 08, Ijomu Oro, Irepodun LGA, Kwara South Shugaban kasa: APC- 98 PDP- 40 Majalisar dattawa: APC- 98 PDP- 43 Majalisar wakilai: APC- 100 PDP- 40 PU 002(Comm pry school) , ward 12, Bode Saadu, Moro LG, Kwara North. Shugaban kasa APC - 406 PDP - 58 AAC - 1 APDA - 1 ANP - 1 DPP - 1 MMN - 1 UDP - 1 Void - 13 Majalisar dattawa: APC - 413 PDP - 57 ADC - 1 ANP - 1 APN - 2 LP - 1 Void - 7 Majalisar wakilai: APC - 420 PDP - 60 ADP - 1 Lai Mohammed ya kawowa APC mazabarsa. APC ta lashe dukkanin kujeru uku a mazabar ministan labaran, PU 06, Oro, Irepodun LGA, jihar Kwara. Shugaban kasa: APC 182 PDP 44. Majalisar dattawa: APC 192 PDP 49. Majalisar wakilai: APC 184 PDP 45. PU 002(Comm pry school) , ward 12, Bode Saadu, Moro LG, Kwara North Shugaban kasa APC - 406 PDP - 58 AAC - 1 APDA - 1 ANP - 1 DPP - 1 MMN - 1 UDP - 1 Void - 13 Majalisar dattawa APC - 413 PDP - 57 ADC - 1 ANP - 1 APN - 2 LP - 1 Void - 7 Majalisar wakilai APC - 420 PDP - 60 ADP - 1 Sakamakon zabe daga mazabar Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki. Shugaban kasa APC 68 PDP 219 Majalisar dattawa APC 60 PDP 269 Majalisar wakilai APC 53 PDP 253 PU 007, Magaji Ward, Agaie LGA, Niger South, Niger State. Shugaban kasa PDP 38 APC179 GDPN 3 APD 1 ANRD 1 ANN 1 PPN 2 NPC 1 Invalid 28 Majalisar dattawa: APC 92 PDP127 PPN 2 ADP 2 NRM 2 ADC 1 PRP 1 NNP 1 Invalid 27 Majalisar wakilai APC 141 PDP 81 LPN 1 PPN 12 PRP 1 NNPP 1 PDM 4 AGA 1 DA 1 NRM 1 LP 1 Invalid 10 Tungan Malefe ward. PU007, Kontagora LGA, Niger north senatorial district. E Shugaban kasa: APC=208 votes PDP=55votes NRM=2votes PPN=1vote INVALID VOTES=62votes Majalisar dattawa: APC=172votes. PDP=106votes PPN=6votes NRM=15votes ADP=1vote ACD=1vote INVALID VOTES=26votes Majalisar wakilai APC=201votes PDP=87votes APGA=2votes PPN=4votes NRM=22votes INVALID VOTES=10votes Shugaban kasa: ACD 1 ADP 3 APA 1 APC 231 DPP 1 PDP 107 PPA 1 Majalisar wakilai: ADP 48 ACD11 ADC 1 APC125 PDP 175 SDP 1 APGA 1 PRP 1 Gwana Umaru Almakura na jihar Nasarawa ya kawo wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mazabarsa. Mazabar Gayan 08 a Kofar Wambai Ward na Lafia Shugaban kasa APC 890 PDP 30 Majalisar dattawa APC 832 PDP 42 Galadima ward PU 004 karamar hukumar Awe jihar Nasarawa. Shugaban kasa: PDD- 103 APC- 203 NRM- 1 Majalisar dattawa PDP-106 APC-193 ZLP-5 APGA-2 PPA-1 Majalisar wakilai PDP-102 APC-196 APGA-1 ZLP-8 PU 006 Ward: Wakma, Lafiya, Jihar Nasarawa Da misalin 5:56 pm, ba a fara kirga kuri'u ba. Kungiyar dauke na maamai na sintiri ba tare da kasancewar tsaro ba. A yau Asabar, 23 ga watan Fabrairu ne 'yan Najeriya ke hada-hadar shirin kada kuri'a don zaben shugabannin da za su ja ragamar kasar a matakin shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki. Da misalin karfe 8:00 na safiyar yau Asabar ake sa ran bude rumfunan babban zaben wanda aka dage tsawon mako daya saboda matsaloli da suka shafi raba kayan zabe a sassan kasar. 'Yan takara sama da 70 ne ke neman darewa kujerar shugaban kasa a zaben, amma Shugaba Muhammadu Buhari na APC, da abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na PDP, ne suka fi jan hankali a zaben shugaban kasa. A wannan babin za mu kawo maku bayanan da ke gudana a jihohin Niger, Kwara da kuma Nasarawa.

Jihar Kwara: Adadin yawan masu rijista ya kasance 1,406,457 inda aka karbi katin zabe 1,149,969 sannan katuna 256,488 na nan a hannun hukumar zabe inda masu shi basu karba ba. Lissafin ya nuna cewa kashi 81.76 cikin 100 da sukayi rijista a jihar Kwara ne suka karbi katunansu. S

hahararrun yan takarar majalisar dokoki a jihar Kwara sune; Kwara ta kudu: Abdulfatah Ahmed na PDP da kuma Ashiru Iyeolola Yisa na APC. Kwara ta tsakiya: Bukola Saraki na PDP da Oloriegbe Yahaya Ibrahim na APC. Kwara ta Arewa: Zakari Mohammed na PDP da kuma Umar Suleiman Sadiq na APC. A jihar Kwara, mun ji cewa rundunar sojin saman Najeriya ta tura jirgin tsaro mai saukar ungulu zuwa Kwara domin sanya ido kan gudanarwar zaben Shugaban kasa da na majalisar dokokin kasar da zai gudana a yau Asabar.

Kwamandan hedkwatar rundunar sojin sama na 203 a Ilorin, Air Commodore Patrick Obeya, ya bayyana hakana taron manema labarai a Ilorin. Yayi bayanin cewa jirgin zai ta sintiri a sama domin samar da tsaro ga mazauna jihar. Obeya ya bukaci mazauna yankin da kada su tsorata, cewa jirgin mai saukar ungulun musamman zai tsaya a wasu wurare. Da misalin karfe 7:21 na safe, a mazabar fadar sarkim Patigi, Jihar Kwara. Yan tsirarun jami’ai ne suka fito.

Har yanzu suna jiran ababen hawa da zai kawo masu kayan zabe. Da misalin karfe 8:23 na safe, ba’a gano jami’an INEC da kayan zabe ba a mazabar Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ba. Mazabar na a kwatas din Agbaji da ke Ilorin, babbar birnin jihar Kwara.

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki isa mazabarsa a Ilorin domin ya kada kuri'a. Hazalika a jihar Kwara an samu rahoton inda ake siyan kuri’u a gaban Alfa Emilola da ke hanyar unguwar Ile Paje da ke Offa. PDP na rudar mutane da kudi yayinda aka fatattaki jami’in APC. Mun samu labarin cewa an kama dan uwan wani jigon PDP a Kwara, Alhaji Ladi Hassan da takardar sakamakon zabe da kuma yiwa jami’an INEC sojan gona

Jihar Nasarawa: Adadin yawan masu rijista ya kasance 1,617,786 inda aka karbi katin zabe 1,442,184, sannan sauran kati 175,602 na nan a hannun hukumar zabe inda masu shi basu karba ba. Lissafin ya nuna cewa kashi 89.15 cikin 100 da sukayi rijista a jihar Nasarawa ne suka karbi katunansu. Shahararrun masu takarar kujerar sanata a jihar sun hada da: Nasarawa ta kudu: Adokwe Suleiman Asonya na jam'iyyar PDP da kuma Umar Tanko Almakura na APC.

Nasarawa ta yamma: Abdullahi Adamu na jam'iyyar APC da kuma Bala Ahmed Aliyu na PDP. Nasarawa ta Arewa: John Micheal Abdul na jam'iyyar PDP da kuma Akwashiki Godiya na APC. Masu zabe a Lafia, jihar Nasarawa sun fara tururuwan fitowa domin kada kuri’unsu na zaben Shugaban kasa da yan majalisa. Mafi akasarin masu zabe sun isa mazabunsu a yankin tun da misalin karfe 7:00 na safe domin bin layi sannan su jira jami’an zabe.

A mazabar Bukan-sidi, an gano masu zabe tsaye cikin zumudi inda wasu suka taru a bangarori daban-daban tare da jami’an tsaro cike domin lura da yadda abubuwa ke gudana. Hakazalika, a lokacin kawo wannan rahoton da misalin 8:18 na safe jami’an zabe basu iso mazabar makarantar Firamare na Lafiya ta gabas ba, sashin Ciroma da wasu mazabu a yankin ba.

Mafi akasarin mutane na nan suna jira ba tare da sun ga wani jami’in zabe ba domin fara kada kuri’arsu. Babu jami’an INEC a Kofa Gayam, karamar hukumar Lafiya inda gwamnan jihar, Umaru Tanko Al-Makura da matarsa Dr Mairo Almakura za su kada kuri’unsu. Daga bisani jami'an INEC sun iso tare da kayan zabe inda jama'a suka kada kuri'unsu a mazabu daban-daban da ke jihar. Sai dai hukumar ta kara lokaci ga wuraren da aka samu jinkiri wajen fara zaben. 


Adadin yawan masu rijista ya kasance 2,390,035 an karbi kati 2,173,204, sannan sauran 216,831 na hannun hukumar zabe. Lissafin ya nuna cewa kashi 91 cikin 100 da sukayi rijista a jihar Niger ne suka karbi katunansu. Shahararrun masu neman takarar kujerar majalisar dokoki sun hada da: Niger ta gabas: Sani Musa (313) daga jam'iyyar APC da kuma Isiyaku Ibrahim daga jam'iyyar PDP. Niger ta Arewa: Abdullahi Aliyu Sabi na APC da kuma Duba Mohammed Sani Niger ta kudu: Mohammed Bima Enagi na APC da kuma Shehu Baba Agaie. An dan samu jinkiri wajen fara zabe saboda rashin isowar jami'an INEC da kayan zabe da wuri a fadin mazabu da dama da ke jihar ta Niger. Tsohon Shugaban kasa, Abdulsalam Abubakar tare da uwargidarsa, Justis Fati Abubakar suyn isa mazabarsu da ke Uphill Water Tank a garin Minna.

Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Niger tare da uwargidarsa Dr. Amina Abubakar Bello sun kada kuri’arsu a mazabar Alkali Mustapha, da ke Kontagora. Da misalin karfe 10:27 na safe an kawo na’urar tantance masu zabe mai aiki a mazabar 005, Hashimi B, karamar hukumar Suleja, kuma dai tuni masu zabe suka fara kada kuri’unsu. Sanarwa: Ci gaba da kasancewa tare da wannan shafin, zamu kasance masu kawo maka karin bayani akai-akai, bukatarmu shine ka yi 'refreshing' shafin lokaci-zuwa-lokaci, domin ci gaba da samun bayanai na gaskiya kan yadda zabukan ke gudana a wadannan jihohin guda ukku.
 

DAGA ISYAKU.COM

 Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN