Type Here to Get Search Results !

Kotu Ta Daure Saurayi Da Ya Yi Lalata Da Gawar Wata Mace Shekara 6 A Kurkuku

An daure wani matashi mai suna Kasim Khuram mai shekara 23 tsawon shekara shida a Kurkuku, bayan ya karya kofar wajen da ake ma gawa ado kafin a bizineta kuma ya yi lalata da gawar wata mata bayan ya karya marfin akwatin gawa da aka saka ta a ciki, ya fito da gawarata ya yi lalata da ita a dakin adon gawa na Co-Operative undertakers a Titin Walsall, Great Barr da ke birnin Birmingham. 

Yayin da yake yanke masa hukunci a kan laifin da ya aikata, Alkalin Kotun Birmingham Crown Court, Judge Melbourne Inman QC ya ce " Wannan ya saba wa duk tunanin natsuwar kwakwalwan bil'adama, ban taba ji ko ganin irin wannan danyen aiki ba, zai yi wuya a iya tunanin irin keta daraja da mutuncin matacce da ka aikata".

Khuram ya shiga dakin yi ma gawa ado ne da karfe 3 na dare, yayin da yake buge da ababen sa maye na Manba da PCP kuma bayan ya kwankwadi Vodka. Ya yamutsa wasu gawaki, ya kuma lalata jikin wasu gawakin mata guda biyu.

Khuram ya ya ce ya yi lalata da gawar wata mace, kuma ya amsa laifin karya kofofin dakin yi ma gawa kawa.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN