Saduwar aure babban ginshiki ne ko kuma a ce jigo ne a cikin
zamantakewar aure wanda idan ana samun tangarda a kai walau ta bangaren mata ko
mijinta, yana da matukar wahala zaman aure ya yi dadi. Wani abin haushi ne, sau
tari za ka ga ana samun matsala ta wurin mata a kan saduwar aure.
Wata matsalarta ba ta cika so ba, wata matsalarta rashin
sanin yadda za ta yi wa maigida domin jindadinsu baki daya, wata matsalarta ma
sai miji ya yi da gaske kafin ya shawo kanta ta amince ya kwanta da ita, wata
kuwa ma ta mayar da saduwar aure kamar wani abu da yake amfanar da miji shi
kadai ban da ita.
To masu irin wannan dabi’ar, su sani cewa ba ga miji kadai
saduwar aure ke amfani ba, har su kansu akwai amfanin da suke samu idan suka yi
saduwa da mazajensu. Filin Taskira ya yi muku nazarin irin muhimmancin da
saduwar aure ke da shi ga mata:
(1) Saduwan aure yana maganin tarin gajiya (stress), idan
kina da wata tattaunawa (interbiew) kamar gobe ko za ki yi magana a wani taron
mutane, bincike ya nuna wadanda ke saduwan aure akalla sau biyu a sati sun fi
yin wani abin kirki.
(2) Saduwan aure yana sanyawa a samu barci maidadi mai kuma
inganci kuma a samu lafiya,saboda zuciya ta samu natsuwa da sauran abubuwa .
(3) Saduwan aure yana maganin ciwon kai, in kina fama da
ciwon kai to saduwa tana maganinsa.
(4) Saduwan aure yana maganin mura wadda sanyi ya kama ki,
sannan yana ba da kariya ga jiki daga kamuwa da sanyi wanda ka iya haifar da
mura.
(5) Saduwan aure yana hana tsufa da wuri, bincike na kiwon
lafiya ya nuna duk matar da ke saduwa, a duk shekara 12 tana komawa ‘yar
shekara 7.
(6) Saduwan aure yana sanyawa mace ta rika samun saukin yin
period (jinin al’ada), da yawa ‘yan mata suna fama da ciwo yayin period amma da
sun yi aure sai su nemi ciwon babu.
(7) Saduwan aure yana canza ma mace yanayin tsarin jikinta
inda kasusuwanta zasu kara girma da wasu sassan jikinta.
(8) Saduwan aure yana kara ma zuciya lafiya, sanin ku ne
ciwon zuciya shi ne ciwon da ya fi kashe mata a duniya, cin abinci mai inganta
lafiya da rage kitse suna taimakawa sannan saduwan aure yana taimakawa wajen
magance zuciya daga kamuwa da ciwo.
(9) Kwanciyar aure yana kara ma mace lafiya a kwakwalwarta
sannan ya cire mata bakin ciki da damuwa ya sanya ta nishadi.
(10) Saduwan aure yana taimakawa wajen inganta lafiyar
‘bladder’ ga mace.
(11) Saduwan aure yana sa mace ta ringa jan hankalin Mijinta
saboda saduwa a kai a kai yana sa kyan fata da bakin gashin kai har da tsayi
ma. ‘Yan’uwa mata sai himmatu wurin gyara abubuwan da za su kyautata wannan
ibada ta aure. Allah ya taimake mu baki daya amin, mu a hadu a mako mai zuwa,
insha Allah.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi