Legit Hausa
Kotun daukaka kara dake birnin Fatakwal ta bada umurnin dakatad da aiwatar da hukuncin babban kotun tarayya da ta bayar na watsi da zabubbukan fidda gwani da jam'iyyar All Progressives Congress, shiyar jihar Ribas ta gudanar.
Tun lokacin, kotun ta haramtawa hukumar gudanar da zabe ta
kasa mai zaman kanta wato INEC sanya jam'iyyar APC da yan takaranta a takardan
kuri'a na jihar RIbas a zaben 2019. A ranan 7 ga watan Junairu, Jastis Kolawole
Omotosho ya yi watsi da dukkan zaben fidda gwani tsakanin bangaren Magnus Abe
da Tonye Cole.
Yanzu haka jihar Zamfara ce ta rage ba tada yan takaran APC
a zaben bana yayinda kotuna biyu daban-daban suka bayar da hukunci masu karo da
juna da hallacin musharakarsu a zabe. Jigo a jam'iyyar APC, Sanata Kabiru
Marafa ya ce Hukumar Zabe mai zaman kanta tayi biyaya da umurnin babban kotun
Abuja inda ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar ta APC ba za ta fitar da 'yan
takara ba.
Sanatan wanda kuma shine Ciyaman din kwamitin majalisar
dattawa a kan albarkatun man fetur ya yi wannan furucin ne yayin hirar da ya yi
da menema labarai a babban birnin tarayya, Abuja. Ya ce INEC ta tsaya a kan
bakar ta na haramtawa jam'iyyar APC reshen Zamfara fitar da 'yan takara saboda
gaza gudanar da zaben fidda gwani a cikin lokacin da aka kayyade mata.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi