Type Here to Get Search Results !

Tsofaffin Janar Guda 71 Sun Goyi Bayan Takaran Shugaba Buhari a 2019


Tsofin janar a rundunar soji ta sama, kasa, da ruwa sun bayyana goyon bayan su ga takarar shugaba Buhari domin sake zama shugaban kasar Najeriya a karo na biyu. A yau, Litinin, ne tsofin janar din sojin su ka shaida wa duniya goyon bayan su ga takarar shugaba Buhari a zaben da za a yi ranar 16 ga watan Fabarairu da mu ke ciki. Tsofin janara-janar din sun hada da ma su mukamin manjo janar 13, Air Vice Marshal (AVM) 8, Rear Admiral 2, birgediya janar 12, Air Commodore 9, Commodore 8 da kuma wasu tsofin shugabannin rundunar soji 17.

Tsohon gwamnan jihar Legas a mulki soji, Birgeiya janar Buba Marwa (mai ritaya) ne ya jagoranci tsofin janar-janar din yayin da su ke bayyana goyon bayan su ga takarar shugaba Buhari a yau. Daga cikin tawagar tsofin janar-janar din akwai Navy Capt Caleb Olubolade, tsohon ministan harkokin 'yan sanda lokacin mulkin Jonathan da kuma tsohon shugaban rundunar sojojin ruwa ta kasa, Admiral Jubril Ayinla. Goyon bayan tsofin sojojin na zuwa ne bayan shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamred Adams Oshiomhole, ya ce manyan tsofin janar na soji da ke kasar nan na kulle-kullen kawo karshen gwamnatin shugaba Buhari ta kowacce hanya.

Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayin gabatar da tutar takara ga gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, dan takarar gwamna a jam'iyyar APC, a filin taro na Malam Aminu Kano da ke Dutse, babban birnin jihar Jigawa. Ya bayyana cewar tspfin janar din sojin na son ganin bayan gwamnatin shugaba Buhari ne saboda irin aiyukan da Buhari ke yi ga jama'ar Najeriya ya saba wa bukatun su. Oshiomhole ya kara da cewar sha'awar shugaba Buhari na son kyautata wa talaka ne babban dalilin da yasa tun a farko tsofin janar na sojin ke murde ma sa zabe tun a baya.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN