• Labaran yau

  An Damke Tsofaffi 9 Bisa Zargin Lalata Da 'Yar Shekara 14

  Alummata.com

  Zuwa yanzu dai mutane 9 ‘yan sanda suka kama bisa laifin lalata wata wata yarinya ‘yar shekara 14 da haihuwa a garin Ingawa ta jihar Kasina.

  Mutanen sun hada da: Ali Isah mai shekaru 68, Ayuba Sada, 65, Danjuma Sale, 62, Ibrahim Sa’idu, 46, Salisu Dahiru 46 da kuma Ibrahim Muhammad, 38.

  Sauran sun hada da: Yahaya Salisu, shekaru 40, Shehu Umar, 55, sai kuma Ibrahim Umar, 45.
  A yayin da aka yi holin mutanen ga manema labarai, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya bayyana cewa muanen wadanda kafataninsu ‘yan garin Ingawa ne, sun yi lalata da yarinyar a lokuta daban-daban.

  Mahaifiyar yarinyar ce dai ta fahimci alamun sauyi a tattare da yarinyar, lamarin da ya sa ta tuhumeta, inda yarinya ta kira sunan Ibrahim a matsayin wanda ke yin lalata da ita.
  Bayan cafke Ibrahim ne tare kuma da tuhumarsa, sai ya ambaci sunayen sauran mutane 8 din da ke yin lalata da yarinyar.

  Daya daga cikin wadanda a ke zargin, Ali Isah, ,ai shekaru 68, ya ce: “Na yi lalata da ita, amma aikin shaidan ne. Na yi nadamar aikata haka. Na yi lalata da ita ne shekaru 3 da suka wuce amma sai ga shi sai yanzu ake tuhumata da laifin.”

  Tuni dai aka gurfanar da mutanen a gaban kotu, kuma kotu za ta fara sauraron karar a ranar 28 ga watan Fabrairu

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An Damke Tsofaffi 9 Bisa Zargin Lalata Da 'Yar Shekara 14 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });