Legit Hausa
Wadanda canjin ya shafa sun hada da Birgediya Janar NJ Okah,
wanda aka dauke daga makarantar fasaha da muhalli ta soji zuwa hedikwatar
rundunar soji a matsayin darektan sashen kula da shige da fice; Birgediya janar
HT Wesley, wanda aka nada a matsayin sabon darekta mai kula da tufafi da
ma’ajiya a hedikwatar rundunar soji; da Birgediya MA Masanawa, wanda aka canja
daga darekta a sashen fasaha da zuwa kwamanda na ACADA.
An canja Birgediya janar HG Tafida daga kula da dakin
kere-kere na sojoji da ke Rigachikun zuwa sashen kula da shige da fice a
hedikwatar rundunar soji. Kazalika an mayar da Birgediya Janar BA Ilori zuwa
sashen sayen kayan amfanin sojoji a hedikwatar rundunar soji.
An mayar da Kanal Onyeama Nwachukwu zuwa hedikwatar rundunar
soji a matsayin mukaddashin darektan sashen labarai na rundunar soji. Kazalika
an nada Kanal Sagir Musa a matsayin sabon mukaddashin kakakin rundunar soji,
yayin da Kanal AA Yusuf zai kasance mataimakin sa Ragowar da canje-canjen su ka
shafa sun hada da kanal AD Isa; sabon mataimakin darekta a rundunar ofireshon
lafiya dole da ke jihar Borno, Kanal S Adama; kwamandan likitocin soji, Kanal
OG Olaniyi; mukaddashin darekta mai kula da sashen kade-kade, Kanal EI Okoro da
Kanal IP Bindul; wadanda aka tura kwalejin horon yaki ta soji a matsayin
ma’aikata da sauran su
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi