INEC jihar Kebbi Ta Yi Taron Fadakarwa Kuma Ta Fara Tantance 'Yan Jarida Don Zaben 2019

Hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Kebb ta gudanar da taron fadakarwa ga Manema labarai kan ka'idodi da 'yan Jarida za su bi domin neman hukumar ta wanzar da sunayensu a cikin tsarinta na sunayen 'yan Jarida da hukumar za ta tantance domin kasancewa a cikin yardaddun 'yan Jarida da za su dau rahotu a ranakun zabe a fadin jihar Kebbi.

Taron wanda aka gudanar da shi a dakin karatu, watau Library na makarantar koyon kiwon lafiya da unguwar zoma na jihar Kebbi, ya sami halarcin Alh Adamu Musa mataimakin Daraktan wayar da kan masu zabe tare da jami'in ilmantarwa tare da watsa labarai na hukumar watau P.A.O Atiku Shekare. Wadannan jami'an sun yi karin haske tare da fayyacewa dalla-dalla abin da kowane 'dan jarida ya kamata ya yi da kuma yadda zai yi.

Daga cikin kafafen watsa labarai da suka sami halartar wurin taron har da Janar manaja na gidan Talabijin na jihar Kebbi, NTA Birnin kebbi da NTA Argungu,Kebbi Radio, Equity Television, Vision FM, Kungiyar 'yan jarida na kasa reshen jihar Kebbi NUJ da ISYAKU.COM.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN