Rundunar tsaro na farin kaya NSCDC a jihar Kebbi, ta damke wasu mutum biyu da ake zargi da tu'ammali tare da mallakar jabun kudi har N300.000 bondur uku na Naira dubu daya kowane.
Kwamandan rundunar NSCDC na jihar Kebbi Samani Muhammed Ringim, ya gabatar da wa'danda ake zargin a gaban manema labaru a hedikwatar rundunar da ke unguwar GRA a garin Birnin kebbi.
Ringim ya ce " Mun yi nassarar kama wadannan mutane ne bayan mun sami bayanan sirri, sakamakon haka na umurci babban jami'i da ke kula da sashen banzatar da dukiyar gwamnati wanda tare da hafsoshin sashen watau Anti Vandal suka yi nassarar kamasu bayan rana ta bace masu".
Wa'danda aka kama su ne Abubakar Shagari dan asalin jihar Sokoto da Atiku Barama daga garin Gwandu na jihar Kebbi.Bayanai sun ce an damke mutanen ne a unguwar Bye Pass da ke garin Birnin kebbi.
Kwamanda Ringim ya ce rundunarsa za ta gurfanar da wa'danda ake zargin a gaban Kuliya da zarar sun kammala bincike.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi