Legit Hausa
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Farfesa Mahmood
Yakubu, yace “wani kudiri na Allah ne kadai zai iya hana gudanar da zaben
Shugaban kasa da na majalisar dokoki da aka dage za a yi a ranar Asabar, 23 ga
watan Fabrairu.
Shugaban na INEC ya bayyana hakan a Abuja yayinda yake
jawabi ga wani taron diflomasiyya da kungiyar masu sanya idanu a zabe na
kasashen duniya a Najeriya. Ikon Allah ne kada zai iya hana zabe a ranar Asabar
23 ga watan Fabrairu.
Ma’aikatar kula da harkokin waje ce ta shirya taron tare da
hadin gwiwar INEC domin tattaunawa tare da abokai da kuma takwarorin Najeriya
kan zaben da aka dage.
Yakubu wanda ya samu wakilcin wani kwamishinar INEC, Dr
Mustapha Lecky ya bayyana cewa hukumar ta tanadi komai domin tabbatar da gudanr
da zaben a ranar Asabar. Shugaban INEC ya bayyana cewa hukumar bata da wani
dalili da take ganin cewa wani abu zai daktar da zaben ranar 23 ga watan
Fabrairu.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi