EFCC ta sanya Daraktan SSS da ke harkalla tare da Lawal Daura a kwana


Legit Hausa

Rahotanni sun kawo cewa jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) sun sheka ruwan tambayoyi da bincike ga mataimakin daraktan kudi na hukumar SSS. Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kafin a fito da Kunle Kadri daga gidan sa, sai da aka cumuimuye shi aka daure masa hannu da ankwa. Kuma yanzu haka ya na can tsare a hedikwatar EFCC, da ke Abuja.

Zuwa yanzu dai jami’an EFCC ba su ce komai dangane da kama jami’in kula da hada-hadar kudade ta SSS ba. Amma dai kwakkwarar majiya ta tabbatar da cewa an gano wata harkalla, asarkala, rub-da-ciki da karma-karma a fannin tasarifin kudade, wadanda aka alakanta cewa da Sanin korarren Daraktan SSS, Lawal Daura aka yi kumbiya-kumbiyar kudaden.

An ce Lawal Daura a yanzu haka ya bude fankamemen ofis a Maitama, cikin Abuja, inda ya ke fantamawa, kuma ya na gudanar da ayyukan tuntuba ga wannan gwamnati. Kadri na daya daga cikin na-hannun-damar Lawal Daura kuma ya amince masa sosai. Ana kuma zargin har yanzu ya na da wata alaka ta boye da suke gudanarwa a asirce shi da Daura.

Majiya ta ce dangantakar ta su ta kut-da-kut ce.’ Masu binciken kwakwaf a EFCC sun tabbatar cewa idan su ka taka ruwan cikin Kadri, to zai amayar da duk abin da ya sani dangane da badakalar da ta dabaibaye wasu kudade har naira bilyan 10.2 da SSS ta fara karba a matsayin kudaden biyan su ladar aikin zabe. An gabatar da kasafin kudain wanda SSS ta ce za a kashe a Hukumar, tun a lokacin Lawal Daura na kan mulki. Amma an fitar da kudin a kwanan baya, lokacin da sabon Daraktan SSS, Yusuf Bichi ya hau mulki.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN