Hausa.leadership.ng
Yanzu haka dai hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta
tabbatar da cewa jam’iyyar APC ba ta da ’yan takara yayin zaben mai zuwa a
jihar Zamfara bayan da ta bayar da sanarwar jerin sunayen halastattun ’yan
takarar da ta ce za su shiga zaben na 2019, wanda za a gudanar a ranar 16 ga
watan nan da kuma 2 ga watan gobe, wato Maris.
Hakan ya biyo bayan yadda INEC din ta ce APC mai mulkin
jihar ba ta gudanar da halastaccen zaben cike gurbi ba har zuwa lokacin da
wa’adin yin hakan ya kare, kamar yadda hukumar ta bayar da umarni. Kodayake dai
wasu bangarori sun daukaka kan wannan mataki da hukumar zaben ta dauka, amma
abin damuwar shi ne, zai yi wahala a kammala karkare wannan takaddama da a
shafe ’yan watanni a na yin ta kafin gudanar da manyan zabukan kasar, wanda hakan
ke nuna cewa, za a iya gudanar da zaben ba tare da ’yan takarar APC ko guda
daya ba.
To, babban abin tashin hankali ga jam’iyyar shi ne, idan har
a ka kuskura a ka gudanar da zabe ba tare da ’yan takarar jam’iyyar sun shiga
ba, to zai yi wahala su iya samun hurumin shigar da kara a gaban kotu kan zaben
da ba a yi shi da su ba. Sai dai kuma idan hakan ta iya wakana har su ka yi
galaba a kotu nan gaba, musamman bayan rantsar da sabuwar gwamnati, to hakan ya
na nufin za a sake rushe dukkanin zababbun jihar kenan, ciki kuwa har da
kakakin majalisar dokokin jihar, wanda kundin tsarin mulki ya ce shi ke da
alhakin rikon jihar a duk lokacin da a rasa kowa a kujerar gwamna da ta
mataimakinsa.
A nan sai dai babban jojin jihar ya amshi riko kenan na
tsawon kwanaki 90 da doka ta tanada, kafin a gudanar da sabon zabe. Kada a
manta da cewa a lokacin da hakan za ta faru, ba APC ke mulkin jihar ba kuma
babu wani nata da ke rike da mukami, illa dai majalisar zartarwa jam’iyyar da
ta kafa gwamnati a wannan zabe da ke tafe, wanda hakan zai iya yin tasiri gare
ta, idan a ka yi amfani da kwamishinonin da a ka nada.
Tambayarmu a nan ita ce, shin wa zai fi amfana, idan APC ba
ta yi takara a Zamfara ba? akwai manyan ’yan takara guda biyu da a ke ganin sun
fi sauran karfi bisa wasu dalilai da wakilinmu a Zamfara ya nazarto ma na.
Yanzu haka tauraruwar ‘yan takara jam’iyyar PDP da NRM da PDP ke haskawa a
jihar Zamfara kuma su ke ta damawarsu babu dare babu rana.
A yanzu haka masu fashin bakin siyasar jihar Zamfara na
ganin cewa wadannan ‘yan takarar ne za su fafata a tsakaninsu matukar APC ba ta
shigo ba. Sanata Saidu Muhammad Dansadau shi ne dan takarar gwamna a jam’iyyar
NRM na jihar Zamfara, yanzu haka ya na daya daga cikin wadanda tauraruwar sa ke
haskawa a jihar da ‘yan takarar majalisar dattawa da ‘yan majalisar dokoki na
kasa da na jiha.
Don yanzu haka babu lungo da sako da ba su kutsa ba kuma
abinda masu ruwa da tsaki a harkar siyasa ke cewa, Sanata Dansadau tauraruwarsa
na haskawa ne sakamakon yadda ya ke kalubalantar gwamnatin jihar Zamfara da ta
tarayya a kan yadda a ke kashe mutane babu dare babu rana a jihar, inda shi ne
kadai ke ta fita cikin kafafen yada labarai ya na kalubalantar gwamnati har ya
na cewa, “ita gwamnatin ta san masu kashe mutane, ta gaza daukar mataki.”
Sanata Kabir Marafa ya bayyana cewa idan APC ba ta samu ‘yan takara ba, to a
matsayinsa na Kabiru zai mara wa daya daga cikin ‘yan takarar da yanzu haka a
ke da su a cikin jihar mai irin akida tasa.
Wasu masana na hasashen cewa Sanata Kabir Marafa zai iya
marawa Sanata Dansadau baya domin akidarsu daya ta adawa da gwamnatin jihar
Zamfara da shi kansa Gwamna Abdulaziz Yari a kan tabarbarewar tsaron jihar da
kuma halin ko’ inkula da a ke ganin ya ke nunawa, idan annoba ta samu al’ummar
jihar. Da alama wannan goyon baya da a ke tsammanin Marafa zai bai wa Dansadau,
zai ba shi tagomashi mai yawa da karkatar da tunanin al’ummar jihar ga goyan
bayansa a zaben gwamna shi da jama’ar shi, don a na ganin da ma burin Sanata
Marafa shi ne ya yi wa Gwamna Yari da mukarrabansa ritayar dole da shi kansa
sanata.
A yanzu haka ga alamu wannan hasashen masana na neman
tabbata, don yanzu haka an fara hada fastar Sanata Dansadau a matsayin dan
takarar gwamna da Muhammad Buhari a matakin shugaban kasa. Lallai wannan wake
da shinkafa tsakanin Tsintsiya da Zuma zai kawo sauyi da fasali a siyasar jihar
Zamfara. A bangare daya kuma, Hon. Bello Muhammad Matawalle, dan takarar gwamna
a jam’iyyar PDP na jihar Zamfara, shi ma yanzu ya na daya daga cikin wadanda
tauraruwarsu ke haskawa ga Zamfarawa, musamman ma wannan ba shi ne karonsa na
farko ba wajen tsaya wa takara a zaben gwamnan jihar Zamfara ba.
Kuma yanzu haka ya shiga yakin sunkuru, babu dare babu rana,
wajen neman ganin ya samu nasara a zabe mai zuwa. Masu Ruwa da tsaki a harkar siyasa
jihar Zamfara su na ganin idan Sanata Kabir Marafa ya marawa Sanata Saidu
Muhammad Dansadau baya sakamakon rashin dan takarar a APC, shi kuma Gwamna Yari
ya mara wa dan takarar na PDP baya, to Matawalle zai iya kai labari, domin da
ma a siyasarsu gida daya su ka fito, wato gidan Sanata Ahmad Sani Yariman
Bakura kuma Allah ya albarkaci Hon Matawalle da kyauta ga al’umma, kamar
Yariman, domin a na ganin shi kullum hannunsa a sake ya ke wanda ba ya
‘kabalu’, kuma irin shi wasu ne jama’a ke bukata.
Hakan kuma karfin da PDP ke da shi a karan-kanta a jihar na
kasancewarta babbar jam’iyyar adawa a jihar tsawon shekara da shekaru zai
taimaka wa tafiyar dan takarar nata, idan APC ba ta yin takara, Wasu masanan na
ganin cewa, kwarjinin Matawalle ga Zamfarawa zai sa ya samu nasarar zabe koda
babu wanda da goya da shi, domin wasu na ganin cewa ba zai aminta da gwamnatin
ta shigo cikinsu ba, don za ta bata ma sa tsari. Idan kuma ta yi ma sa kutse
zai samu matsala ba, tunda dai dan takarar gwamnati ne ba a so kuma shi an san
ba na gwamnati ba ne, domin a zaben da ya gabata da shi ne Gwamna Yari ya
fafata, wanda ba don guguwar Buhariyya da APC ba, a na ganin Yari ba zai kai
labari a 2015 ba. Yanzu dai kallo ya koma sama tunda shaho ya dau giwa!
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi