Hausa.leadership.ng
Kungiyoyin tuntuba na al’ummun Nijeriya da suka hada da
kungiyar dattawan Yarbawa ta Afenifere, da Ohanaeze Ndigbo ta kabilar Igbo, da
kuma kungiyar dattawan arewa wato (Northern Elders Forum) sai kungiyar arewa
masu tsakiya da ta hadin kan ‘yan Neja-delta, sun ayyana dan takarar shugaban
kasa karkashin inuwar jam’iyyar PDP, wato Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan
takarar da zasu goya ma baya.
Kungiyoyin suna cikin tsakiyar gabatar da taron nasu ne a
babban otel din Sheraton da ke Abuja, inda suka ayyana Alhaji Atiku Abubakar a
matsayin wanda yafi cancanta da shugabancin kasar nan, don haka dole su fito
karara don ayyana shi a matsayin wanda zasu goya ma baya a zabukkan shekarar
2019.
Jagororin kungiyoyin
sun hada da Cif Ayo Adebanjo, Cif Nnia Nwodo, Farfesa Ango Abdullahi, Cif Edwin
Clark da kuma Dakta Bitrus Pogu, sun bukaci ‘yan Nijeriya da su zabi jami’iyyar
PDP a zaben da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu da muke fuskanta.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi