Type Here to Get Search Results !

Yariman Saudiyya mai jiran gado ya hau rufin dakin Ka'aba

Legit Hausa
Yariman kasar Saudiyya mai jiran gado Muhammad bin Salman ya hau saman rufin dakin Ka'aba a lokacin da ya kai ziyara garin Makkah mai tsarki.

An tattaro cewa, Yariman ya ziyarci garin Makkah ne saboda ya duba sabbin ayyukan da ake gudanarwa a Dakin Ka'aba.

Bin Salman da ya halarci wanke Dakin Ka'aba da aka saba yi tare da jami'an tsaro 600 dake kare shi ya fara sumbatar Hajarul Aswad inda daga nan kuma ya hau matattakalar tare da shiga cikin dakin Ka'aba.

Yarima bin Salman ya yi Sallah a cikin Ka'aba inda ya dauki wani tsumma tare da yin goge-goge, sannan kuma sai ya hau saman rufin Dakin Mai Tsarki wanda abu ne da ba a saba gani ba.
Hawan Yariman saman Dakin Ka'aba ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta na yanar gizo.

An samu tarihin cewar daga cikin Halifofin Daular Abbasiyya Abu Ja'afar Al-Mansur ya taba hawa rufin Dakin.

A yanzu dai ma'aikata na hawa saman Dakin don tsaftace shi a lokacin da aka yi ruwan sama ko kuma za a sauya rig
Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN