Babu yadda za a gudanar da zabe a jihar Zamfara ba tare da 'yan takaran APC ba - Gwamna Yari

Gwamna Abdulazeez Yari ya yi barazanar cewa babu yadda za a gudanar da zabe a jihar Zamfara matukar hukumar zabe INEC bata saka sunayen yan takaran jam'iyar APC ba a jerin sunayen 'yan takara da za su yi zabe a jihar.

Yari ya yi wannan zancen ne a garin Talata Mafara ranar Juma'a yayin yakin neman zabe a karamar hukumar a gaban dimbin magoya bayan jam'iyar APC.

Gwamnan ya ce " Babu yadda za a gudanar da zabuka a jihar Zamfara ba tare da yan takaran jam'iyar APC ba duk da cewa aabban Kotun jihar Zamfara ta tabbatar da APC ta gudanar da zaben fitar da gwani".
 
" Mun dogara ne da hukuncin da babban Kotun Zamfara ta yanke kan shari'ar cewa APC ta gudanar da zaben fitar da gwani a Zamfara kuma ta bayar da umarni cewa INEC ta saka sunayen 'yan takarar APC a zabukan da za a yi".

Idan dai baku manta ba, INEC ta ce APC bata gudanar da zaben fitar da gwani ba a Zamfara, sakamakon haka bata gabatar da sunayen 'yan takaranta ba ga INEC kafin wa'adin ranar 7 ga watan Oktoba 2019.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post