Leadreship Hausa
Talauci na daya daga cikin matsalolin da wannan gwamnati ta
shugaban kasa Muhammadu Buhari ta haifar a Nijeriya da nufin kowa ya tashi a
tsaye ya rike kansa idan zai iya ko ba zai iyaba. Lamarin da mutane masoya
wannan gwamnati ke ganin kamar wani abin alfahari ne a ce kowa ya koma gona ko
kuma ya koma kan bola tattara kayan shara domin neman abinci daga cikin bolar,
yadda idan an rasa kayan bola matasa ke wucewa satar kayan wanda su ka yi sake.
Kasashen da ke irin wannan tsari kamar su Jamus ko Indiya ko
China da makamantan su, kasashene da suka ginu a kan wannan hanya kuma su na da
masana’antu da bayar da tallafi kan kiwon lafiya da ilmi da samar da abinci da
sauran kayan more rayuwa na yau da kullum har da inshore da alawus ga marasa
aikin yi. Sabanin a Nijeriya da idan mutum ya shiga wahala musamman a wannan
lokaci sai ko ya nemi rayuwa ko da tsiya ko da arziki, saboda rashin abin yi da
kuma rashin tallafi musamman a wannan lokaci ba kamar yadda a ka saba a
gwamnatocin baya inda ake agazawa a fannoni da daman a rayuwa ba. Duk da irin
wahalar da ake sha a kasar nan kashi 60 cikin dari na talakan wanda ke shan
wahala idan ka ce masa gwamnatin Buhari ta gaza wani yanzu zai ci mutuncin ka.
Yadda hatta wannan rubutu da na ke yi idan na biye irin
wadannan mutane da tuni na daina. Amma kasancewar masu bugo waya su gode su
nuna jin dadi sun fi yawa, kuma da dama sun fahimci gaskiya muke fada, shi yasa
nake ci gaba da wannan rubutu duk da irin cin zarafin tura sakonni da wasu ke
yi. Amma wasu idan sun kira waya sai su ce munyarda gaskiya kake fada amma ba
laifin Buhari ba ne na wanda suka gabace shine don haka zai gyara idan ya dawo
na kasan sa ke zagon kasa basa son sa basa son kasar. Hakan ya sa wasu ke yin
kirari da cewa Buhari Annabin wawaye, ko raba talaka da Buhari sai Allah.
Mun ji mun yarda amma kowa ya rubuta ya ajiye akwai lokacin
da zai zo dole yadda talaka ya ji a jikinsa haka suma shugabannin za su ji a
jikin su, domin idan manya masu hankali sun ci gaba da nuna soyayya da samina
wa adana wa Buhari, matasa a karshe talauci zai sa su bijiriwa gwamnati sai
yadda Allah yasa hali ya kasance.
Saboda kasa kamar gidane idan mutum bai yarda ba ya daina
kai cefane gidansa ya ce iyalensa kowa ya tashi ya dogara da kansa na tsawon
wata guda, yaga yadda za su lalace, ban zaci za a kai wata guda ba za a samu
karuwai da barayi a cikin gidan kamar yadda ke faruwa yanzu a Nijeriya yadda a
nan gaba za a sha wahala kafin a gyara tunanin matasa da ‘yan matan da su ka
zama barayi ko ‘yan shaye shaye ko sara suka, daga nan za a fahimci ashe Allah
ya rufawa mutane asiri Buhari yazo ya kuntata ya tona musu asiri.
Saboda a
kullum haifar yara ake yi kuma kashe kudi ake yi a kansu wajen yin karatu amma
babu wani shiri na gaskiya domin basu aikin daya dace da ilmin su sai N-power
wanda har zuwa wannan lokaci ban yi zaton an dauki mutane dubu dari a wannan
shiri ba. Kuma me ake zato yaro ya yi karatu ka ba shi da aiki shekara biyu
kana bashi dubu talatin ya yi aure ya fara tara iyali ka katse kace ya tafi ya
nemi abin yi, wanda na san shi lokacin da ya yi nasa karatun yana gamawa ga
aiki wani lokaci har da abin hawa.
Daga nan sai gaba da zagon kasa tsakanin matashi da gwamnati su kullu. Kuma abin takaici wannan yaudarar duk a na yi wa masu karatune, jahilai da ba su samu karatu ba ba wani tanadi da a ke yi mu su sai basu kayan maye su bi ‘yan siyasa wanda daga bisani idan su ka samu mugaye su ka ba su makami za su aikata komai kamar yadda ke faruwa a wasu jihohi.
Daga nan sai gaba da zagon kasa tsakanin matashi da gwamnati su kullu. Kuma abin takaici wannan yaudarar duk a na yi wa masu karatune, jahilai da ba su samu karatu ba ba wani tanadi da a ke yi mu su sai basu kayan maye su bi ‘yan siyasa wanda daga bisani idan su ka samu mugaye su ka ba su makami za su aikata komai kamar yadda ke faruwa a wasu jihohi.
Hakan daga bisani zai kasance idan su na tsoron jami’an
tsaro za su daina idan wahala ta yi wahala kuma sai kurum su zaman ‘yan tawaye
sai neman wargaza kasa ta kowane hali, da fatar Allah ya kiyaye ya kawo mana
karshen wannan lamari yasa shugabannin su hankalta su koma hanyar gaskiya.
Bayan haka akwai matsaloli irin na lalacewar tarbiyya da neman abinci ta kowace
hanya halas ko haram, ga barazana ta rashin tabbas yadda kowa idan ya wayi gari
bai san me gobe za ta haifar ba, musamman yadda a wasu lokuta wanda ke ci ya
ciyar da wani yanzu an wayi gari cikin kasa da shekaru hudu wanda ke taimakon
wasu da abinci da kayan bukata yanzu an wayi gari shi ne ke neman taimako.
Saboda ya tara iyali, amma yanayin da a ka shiga ya sa abin
hannun sa ya kare ba yadda zai yi saboda idan zai aura ko zai auras ko zai yi
jinya ko wata hidima mai cin kudi sai ya sayar da kadara har an kai wani
matsayi da yanzu babu kadarar da zai sayar ya koma maula ko bara. Yadda a
masallaci daya idan an idar da sallah sai mutum goma ko fiye su tashi suna bara
kowa na fadar matsalarsa babu mai jin ta wani saboda tsabar damuwa da talauci
da suka dabaibaye mutane.
Mazauna karkara kuma kullum tura yaransu suke yi birane
aikin wahala ko almajiranci don neman abin sawa a baka, har ya zamo iyaye
kamara yaran sun dame su basu ki sun mutu ba ko sun bar inda suke don su huta
da dawainiyar su. Maza sun lalace sun zama sai shaye shaye da ta’adda wasu ‘yan
mata sun zamo karuwai kai har matan aure sun lalace. Tun masallatai na hana
bara har sun kai ga mai ganin laifin wanda ke bara shima an wayi gari talauci
ya addabe shi ji yake yi kamar ya yi barar, illa iyaka idan kana da masu
tallafa ma daga yara ko makusanta shikenan za ka samu saukin lamarin.
Wani abin mamaki ya faru a wata unguwa yadda wani mai hali
abin ya hannu ya kare, duk wata hanya da ya ke nema ta rufe. Aka wayi gari ba abin
da za a ci a gidansa Allah ya jarrabe shi yaga babu yadda zai yi, bayan an yi
sallah a masallacin unguwa ya tashi ya fadawa mutane halin da ake ciki ga yara
yau kwanaki ba wanda ya ci ya koshi, sai ya fashe da kuka haka mutane su ka ta
tallafawa su ma wasu na kuka.
Daga nan akwai wani malami ya kira shi gidansa ya auna masa
mudu biyar na gari mudu biyar na shinkafa ya bashi naira dubu biyu yana karba
sai ya fashe da kuka yace yau ni da ke bayarwa ni ne na koma mabaraci sai ya
fadi har asibiti tsabar takaici, duk wanda ke ganin ba haka ba yazo zan kai shi
har inda abin ya faru. A cikin kasuwar wunti da ke Bauchi akwai limamin wani
masallaci da ya dinga wa’azi da yiwa Buhari kamfen a 2015 har aka rika tsanar
sa, amma sai aka wayi gari a bara jarinsa ya karye babu abin da yake yi sai a
zo kasuwa a zauna a tashi hannu wofi.
Masallaci kuma ba abin da ake samu sai ko ya bada sallah
kowa ya tafi, aka wayi gari ya shiga damuwa wata rana an tayar masa ikama ya
tsaya zai ja sallah sai jiri ya kwashe shi aka kama shi aka zaunar aka masa
fifita ya dawo hayyacin sa, ya ce wallahi kwana uku kenan baici abinci ya koshi
ba, don bai san yaya ma ta ke yi da yara ba idan yayi asuba ya fito kasuwa sai
bayan isha yake komawa. Nan a ka nemi taimako aka tara dubu ashirin da bakwai a
ka saya masa buhun shinkafa aka bashi sauran canjin.
Wallahi a nan Bauchi akwai matar da taje kasuwar Central ta
sayi shinkaf tara da yarinyarta yayayya sai ta duba jaka kamar da kudi daga
karshe ta ce tabar kayan da ta saya a wani shago yarinya ta jirata a wajen tana
zuwa ta tafi da shinkafar ashe gida ta wuce.
Mutum ya jira har ya gaji sai suka sa yarinya a gaba har
gida suka yi sallama da ta leko taga yarinya da mutane tace su shiga, sai ta
nuna musu shinkafa a kan wuta ga yara gewaye da murhu suna jira tace wallahi ba
yadda za ta yi yau kwanaki ta rasa me za taba yaran sun dameta da kuka duk masu
taimaka mata sun gaji mijinsu ya gudu ya barsu don haka dole tasa ta daukar
wannan matsaya, haka ‘yan kasuwa suka tausaya su ka ba ta yarinyarta suka tafi
suka barta. Irin wannan misali idan zan bayar dasu a cikin Bauchi kurum zan
bada masu yawa game da kuncin rayuwa abin da ke jefa mutane cikin matsala.
A takaice akwai labarin da na karanta a kudancin kasar nan
kwanaki an kama gungun ‘yan fashi da makami yawancin su sun yi karatu kusan
kowa yana da takardar digiri yayi NYSC ba abin yi. Akwai wanda yace ya nemi
aiki sama da sau dari ya je jarrabawar daukar aiki yafi sau talatin bai samu
aiki ba. Nan take aka ce kwamishinan ‘yan sandan yasa aka rika tafiya dasu daya
bayan daya gidajensu kowa yana dauko takardar karatunsa, haka ya hallara su ya
tafi ya kaisu gaban gwamna daga nan aka fara neman yadda za a taimaka, wannan
wace irin kasa ce don Allah. Allah ya taimaka mana ya hada mu da masu tausayi
masu kaunar mu ba sai wani makon.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi