Wasu da ba'a san ko su waye ba sun kashe jami'an hukumar hana sha da tu'ammali da miyagun kwayoyi NDLEA guda hudu yayin da suke gudanar da aikinsu a jihar Ondo ranar Lahadi.
Majiyar ISYAKU.COM ta ce wasu mutane ne a kan babura suka nufi wajen da jami'an suke gudanar da aikin tsayar da ababen hawa suna bincike, sai suka bude masu wuta da bindigogi, kuma suka kone motar jami'an kirar Hilux.
Daya daga cikin hafsoshin guda biyar ya tsira da ransa, amma hudu daga cikinsu sun mutu nan take. Tuni sauran jami'an tsaro suka isa wajen da lamarin ya faru domin bincike da farautar wadanda suka aiikata wannan danyen aiki duba da cewa maharan sun yi awon gaba da bindigogin jami'an na NDLEA.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi